Kungiyar Kiristocin Arewa (NCA) ta bayyana goyon bayanta ga taron Limaman mabiya Katolika na Najeriya bayan ganawarsu da Shugaba Bola Tinubu, tare da sukar Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Daniel Bwala.
Shugaban kungiyar, Fasto Joseph Hayab, ya ce kalaman da limaman suka yi sun shafi matsalolin tsaro, tattalin arziki da rayuwar 'yan Najeriya baki ɗaya, ba wai na Katolika kaɗai ba.
Hayab ya zargi Bwala da ƙoƙarin haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin mabiya addinin Kirista, yana mai jaddada cewa NCA ta ƙunshi mambobi daga ɗariku daban-daban da suka haɗa da Katolika, Anglican, Baptist, ECWA, Methodist da Pentecikostal.
Ya kuma ce ya kamata gwamnatin tarayya ta karɓi shawarwarin limaman cikin girmamawa maimakon mayar da martani da zai ƙara raba kan al'umma, yana mai gargadin cewa matsalolin da ƙasar ke fuskanta za su shafi kowa idan ba a magance su cikin gaggawa ba.
