Biyo bayan shari'ar da FIFA ta yi dangane da rikicin da ya ɓarke tsakanin 'yan wasan Argentina da na Spain bayan da aka tashi wasan zagayen ƙarshe na gasar cin kofin duniya a Amurika, inda Argentina ta sha kashi a hannun Sifaniya wanda hakan ya jawo hatsaniya har ma da buge-buge.
Yau hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ta wallafa sunayen 'yan wasan da ya kama da lafi da kuma hukuncin da ta yanke wa kowane ɗan wasa.
Bayan nan hukumar ta yanke hukuncin ƙungiyar ta Ajantina za ta biya tarar zunzurutun kuɗi Dalar Amirka 321,000 tare da umartarsu da buga wasanni guda biyu a jere tare da rabin magoya bayanta ba kamar yadda ta saba.
Su kuwa 'yan wasan da abin ya shafa sun haɗa da:
to play next two home matches with a limited number of spectators (50%) following World Cup clashes.
An dakatar da ɗan wasan Ajantina Leandro Paredes, daga buga wasanni goma (10) a jere tare da cin sa tarar dalar Amirka $90.000.
Shi kuwa Nahuel Molina, na ƙasar Ajantina an dakatar da shi daga buga wasanni bakwai tare da cin sa tarar dalar Amirka $90.000.
Yayin da aka dakatar da ɗan wasan ƙasar Sifaniya Pablo Gavi, wasa ɗaya da tarar kuɗi dalar Amurika $30.000.
Shi maThiago Almada, na ƙasar Ajantina an dakatar da shi daga buga wasa ɗaya tare da cin sa tarar dalar Amirka $30.000.
A ɓangaren masu horaswa na Ajantina da abin ya rutsa da su, akwai Roberto Ayala wanda aka dakatar da shi wasanni uku (3).
Sai kuma Pablo Martín Páez Gavira da aka dakatar da shi wasa guda.