Shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshksian ya ce lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen yaƙin da ƙasar ke yi da Amurka kasancewar a yanzu Iran ɗin ce a ‘sama’.
Pezeshksian ya ce: “yanzu ne ya fi cancanta a kawo ƙarshen yaƙin, yayin da muke da tasiri, muke da sauran mutunci kuma duk duniya aka amince cewa mun yi nasara, sannan ya jaddada cewa Amurka ta saɓa wa dokoki ta hanyar kai hare-hare kan makarantu da asibitoci da kayan amfanin al’umma, “kuma duniya ta tsane ta.”Pezeshksian ya soki lamirin waɗanda ya ce “ba su san abin da yake faruwa ba” kuma ba su san halin da gwamnati da kwamandojin sojin ƙasar da majalisar dokoki ke ciki ba. Suna magana ba tare da sanin wahalar da ake ciki ba.”
Sai dai shugaban ya ce kalamansa ba suna nufin miƙa wuya ba ne: “Ba za mu miƙa wuya ba ta kowane irin fanni, babu tantama a kan hakan. Za mu tunkare su har lokacin da numfashinmu zai fita kuma za mu azabtar da su.”
Kalaman na shugaban Iran na zuwa ne yayin da gwamnatin Amurka ke sauya salon yaƙin, inda a yanzu take ƙokarin komawa kan matsi na tattalin arziƙi.