An kaddamar da sabon littafin Sahihul Buhari da aka fassara daga harshen Larabci zuwa Hausa , wanda Alkali Ahmad Zarrouq Idris Kabara ya wallafa.
An gudanar da taron kaddamar da littafin ne a ranar Lahadi, 16 ga Agusta, 2026, inda malamai da masana da sauran al’umma suka halarta.
Da yake gabatar da nasa jawabin a wajen taron, Farfesa Matabuli Shehu Kabara ya yi bayani kan yadda aka gaji aikin fassarar Sahihul Buhari daga marigayi Shehu Nasiru Kabara, tare da bayyana irin daraja da muhimmancin da wannan littafi yake da shi a wurin Shehu Nasiru Kabara.
Shi ma Farfesa Umar Sani Fagge ya gabatar da nasa jawabin, inda ya yaba da aikin da aka gudanar, yana mai cewa fassarar Sahihul Bukhari zuwa Hausar Boko ba ƙaramin aiki ba ne, musamman duba da irin gudummawar da malamai suka bayar wajen yada ilimi.
Marubucin littafin, Alkali Ahmad Zarrouq Idris Kabara, ya yi dogon bayani kan yadda ya samu ilimin karatun Sahihul Bukhari daga Shehu Nasiru Kabara. Ya bayyana cewa, idan aka lissafa jerin malamai daga Imam Buhari zuwa gare shi, akwai mutane 23 a tsakaninsu.
Ya kuma bayyana cewa ya gabatar da karatun nasa a gaban Shehu Nasiru Kabara tun a shekarar 1996.
A nasa jawabin, Uban taron kuma Shugaban Darikar Qadiriyya na Afirka, Sheikh Qaribullahi Sheikh Nasiru Kabara, ya yaba matuka da wannan gagarumin aiki.
Sheikh Qaribullahi ya bayyana cewa malamai ya kamata su kasance cikin al’umma, su yi duk abin da zai taimaka wajen ci gaban al’umma da yada ilimi.
