Fasto Ya Mutu Sakamakon Cizon Maciji a Jihar Plateau

An tabbatar da mutuwar wani matashin Fasto mai suna Rev. Nankur Peter Kundul, bayan maciji mai dafi ya sare shi yayin da ya ke gudanar da aikin wa’azi a ƙauyen Boltim, Gundumar Gamakai, Ƙaramar Hukumar Langtang South ta Jihar Plateau.

Plateau

Rev. Kundul, wanda fasto ne a cocin Church of Christ in Nations (COCIN), na zaune yankin ne a matsayin mishan.

Wani abokin aikinsa, Fasto Rinkyer Asaph, ne ya bayyana rasuwar a shafukan sada zumunta na Christian Daily International a ranar Litinin. 

Ya ce yankin da marigayin ke gudanar da aikin mishan na da  matsalar yawaitar macizai masu dafi, waɗanda sun dade su na kisa.

Asaph ya bayyana cewa abokinsa ya rasu ne sakamakon cizon maciji a Sabon Gida Clinic, kuma a cikin mako guda kacal, akalla wasu Kiristoci biyu sun riga sun mutu sakamakon irin wannan cizon macijin.

Post a Comment

Previous Post Next Post