Alkalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari’a Faruku Bunza, ya samu ’yanci bayan ya shafe mako guda a hannun masu garkuwa da shi.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da hakan a ranar Litinin, inda ta bayyana cewa an saki alkalin, wanda aka yi garkuwa da shi daga gidansa da ke ƙaramar hukumar Bunza a ranar 26 ga Yulin 2026.
Rundunar ta ce iyalansa da kuma Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kebbi sun tabbatar da cewa an sake shi.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Bashir Usman, ya ce ko da yake masu garkuwa da mutanen sun buƙaci a biya kuɗin fansa, rundunar ta ci gaba da tsayawa kan matsayarta na kin biyan fansa.
Bayan sakin alkalin, rundunar ’yan sanda tare da sauran hukumomin tsaro sun ƙara ƙaimi wajen gudanar da bincike domin gano da kuma kama waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Rundunar ta buƙaci jama’a su bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen binciken, tana mai tabbatar da cewa za a kiyaye sirrin duk wanda ya bayar da bayanai.
Haka kuma ta yaba wa jama’a da sauran hukumomin tsaro bisa haɗin kan da suka bayar a lokacin da alkalin yake tsare, tare da tabbatar da aniyarta na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
Wani ɗan uwan alkalin ya tabbatar da sakin nasa, yana mai cewa ya koma gida lafiya sa’o’i kaɗan kafin fitar da wannan rahoto.
Ya ce iyalan suna cikin farin ciki da godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa dawowarsa gida lafiya bayan mako guda a hannun masu garkuwa da shi.
Ya kuma gode wa bangaren shari’a na jihar, hukumomin tsaro, gwamnatin jihar, abokai da al’ummar Kebbi bisa addu’o’i, saƙonnin ƙarfafawa da sauran nau’o’in tallafin da suka ba su a lokacin wannan ƙalubale.
Sai dai iyalan sun ƙi bayyana yadda aka samu sakin alkalin, suna cewa za su bayyana cikakkun bayanai nan gaba.
An yi garkuwa da Mai Shari’a Bunza ne a makon da ya gabata a ƙaramar hukumar Bunza ta Jihar Kebbi, lamarin da ya jawo tofin Allah tsine daga sassa daban-daban tare da ƙara nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a jihar.
Sakin alkalin ya kawo sauƙi ga bangaren shari’a, iyalansa da al’ummar Jihar Kebbi, waɗanda suka daɗe suna jiran labarin dawowarsa gida lafiya.