Gianni Infantino Na Ci Gaba Da Neman Goyon Bayan Donald Trump

Shugaban Ƙunggiyar Ƙwallon ƙafa Ta Duniya (FIFA) Gianni Infantino na neman agajin shugaban ƙasar Amurka Donald Trump yayin da al'umma ke ci gaba da suka akan salon shugabancinsa, musamman a 'yan kwanakin nan.

Shugaban na FIFA, Gianni ya fara neman goyon bayan gwamnatin Shugaban ƙasar Amurka Trump bayan da ya fara fuskantar ƙarin suka sakamakon wani sabon shiri mai cike da ce-ce-ku-ce na sayar da wani kaso na  kasuwancin Gasar Kofin Duniya, wanda da yawan mutane suka alaƙanta sayen hannun jarin ga shi Trump ɗin.

Wani rahoto daga jaridar New York Post, wanda ta wallafa a yau Litinin, Infantino ya yi ƙoƙari sau da dama wajen ganin ya tuntuɓi Trump ta wayar tarho, sai dai kash hakan bai yi nasara ba, duk da cewa an yi watsi da shirin cefanar da wani kaso na gasar a ranar Juma'ar da ta gabata.

Da yawan majiyoyi musamman waɗanda suka san yadda abin ya faru sun shaida wa jaridar cewa, shugaban FIFA ya fara jin tamkar ya rasa mutanen da ke goya masa baya, a lokacin da suke kan wannan shiri.

Sai dai kawo yanzu da ake haɗa wannan rahoton babu wani saƙo da ya fita daga sashen hukumar ta FIFA na neman ƙarin bayani.

Post a Comment

Previous Post Next Post