A safiyar yau Litinin ne 02/08/2026, da misalin ƙarfe shida na safe (6:00am) Mai shari'a Faruk Hassan Bunza ya dawo cikin iyalansa.
A wata fira da aka yi da wani makusancin alƙalin, a gidan talabijin na DCL. Ya bayyana wa manema labarai cewa, an sako shi ne a yau Litinin da sanyi. Safiya wajajen ƙarfe 6 zuwa 7 na safe. Kuma alhamdulillah ya dawo cikin ƙoshin lafiya kamar yadda aka ɗauke shi. Ya tabbatar da cewa babu wani rauni a jikinsa a lokacin da suka haɗu da shi. Sai dai ya zuwa yanzu yana asibiti tare da 'yan sanda domin duba lafiyarsa da kuma ci gaba da bincike.
A fitar tasa, ya bayyana cewa, mai shari'ar ya dawo a cikin motar haya, wadda ta kawo shi har ƙofar gida. Sai dai bai bayyana yadda aka yi har ya haɗu da motar da ta kawo shi gidan ba. Amma dai ya ce lallai shi yana cikin waɗanda suka kai kuɗin fansa kimanin ₦50,000,000, wanda a lokacin ma da suke kan hanyarsu ta kai kuɗin ɓarayin suka kira su, sannan suka ba su sallahu na su taho masu da maltina da kuma Dudu guda biyar-biyar. Wanda suka shanye su a gabansu.
"Mun kai kuɗin fansar ne daga nan Birnin Kebbi, kuma duka tsawon tafiyar ba ta wuce kilomita saba'in ba (70km). Ya ƙara da cewa, mutane 5 ne muka damƙa wa kuɗin fansar a ranar Juma'a 31-07-2026 kamar yadda aka tsada ce da su. Sai dai ba su ba mu alƙalin mun taho da shi ba. Kwatsam sai ga shi da safiyar yau Litinin ya dawo gida a motar haya."