Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi watsi da rahotannin gwamnatin APC da ke cewa tattalin arziƙin ƙasar Nijeriya na haɓaka, wanda ya bayyana alƙaluman da gwamnatin ta fitar a matsayin wasu abubuwa da ba su tafiya da halin da talakawa ke ciki.

Atiku ya ɗora alhakin hakan bisa tsare-tsaren gwamnatin, wanda ya bayyana janye tallafin mai da kuma tsadar kuɗin wutar lantarki a matsayin manyan dalilai da suka jefa kamfanonin cikin mawuyacin hali. Bayanan Atikun ya gina bayanansa ne a kan rahotannin da Ƙungiyar Masana'antu ta Ƙasa (MAN) ta fitar.

Daga ƙarshe, ɗan takarar jam'iyyar ADC na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya sake yin kira ga gwamnatin tarayya da ta sake duba tsare-tsarenta domin ganin ta ceto ɓangaren masana'antu daga tangal-tangal da suke tare da kuma yin ƙoƙari wajen rage raɗaɗin da al'umma ke ciki.