An Tura Wa Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar ADC Makudan Kudade Da Sunan Gudummuwar Kamfe

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan wasu maƙudan kuɗaɗe da aka tura masa a cikin ɗaya daga cikin asusunsa na sirri ba tare da sahhalewarsa ba.

An samu labarin shigar wasu maƙudan kuɗaɗe da ba a bayyana adadinsu ba, a ɗaya daga cikin asusun sirri na ajiyar bankin Atiku Abubakar, A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a yau Juma'a. Sanarwar ta bayyana cewa, wani mutum ne da ba a san ko wanene ba ne ya tura kuɗin tare da rubuta cewa: "Contribution Electioneering Campaign." A matsayin dalilin tura kuɗaɗen.

Atiku ya bayyana cewa, bai nema ba kuma bai da wani daga cikin ma'aikatansa ya nemi wata gudunmuwa ba. Ɗan takarar shugaban ƙasar ya bayyana damuwarsa ƙarara ta yadda har sirrin lambobin asusun ajiyar nashi ya fita waje, har aka samu damar tura wani abu a ciki, ba tare da sahhalewarsa ba. Ya kuma ƙara da cewa idan har bayanan sirrin asusun tsohon mataimakin shugaban ƙasa za su iya shiga hannun wasu ba tare da izini ba, to lallai hakan na nuna cewa sirrin kuɗaɗen 'yan Nijeriya na cikin haɗari da taraddadi.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi zargin cewa wataƙila wasu masu damar samun bayanan sirri ne suka fitar da su domin biyan wata bukata ta ƙashin kansu, ya kuma yi gargaɗin cewa hakan na iya jefa masu asusun cikin haɗarin masu garkuwa da mutane, 'yan ta'adda, 'yan bindiga da masu damfara, da sauran miyagun mutane.

Ya bayyana cewa, an riga da an shigar da batun ga hukumomin tsaro tare kuma da sanar da al'umma halin da ake ciki domin gudun yarfe na siyasa, tare da yin kira da kar wannan ya sa wani abu ya shiga tsakanin masoyansa da shirye-shiryen zaɓen 2027.

Post a Comment

Previous Post Next Post