Gwamnatun Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai girma Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ɗaurin auren gata na zawarawa da ’yan mata guda 1,500 a Masallacin Sarki da ke cikin birnin Kano, ƙarƙashin shirin gwamnatin jihar da Hukumar Hisbah ta Kano ta gudanar.
An gabatar da ɗaurin auren ne a yau Juma'a 7/08/2026 a masallacin mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II. Gwamnan ya bayyana shirin auren gatan a matsayin wani tsari na jin ƙai da tallafa wa al’umma, waɗanda ke da nufin dawo da fata, ƙarfafa zaman iyali da kuma inganta kyawawan ɗabi’u a cikin al’umma.
Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf shi ya wakilci angon farko, wato Malam Haruna wanda aka kashe matarsa da 'ya'yansu a wani abin alhinin da ya afku a Kano, inda ya nemi auren amaryar daga hannun waliyyinta, Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II, wanda ya amince da buƙatar bisa tanadin addinin Musulunci.
Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa an tantance dukkan waɗanda suka amfana da shirin. Inda a ciki aka cire wasu mutane 200 da aka same su da rashin lafiya bayan karɓar sakamakon gwajin da aka yi kafin auren, sai dai ya bayyana cewa, za a iya dawo da su cikin tsarin matuƙar sun samu ingantacciyar lafiya. Ya kuma ce akwai wasu matan da su ma aka cire su daga tsarin auren gata sakamakon samunsu da aka yi da juna biyu.
Babban Limamin Kano, Farfesa Sani Zahraddeen, ya jagoranci addu’o’in neman shiriya da albarka da zaman lafiya ga sabbin ma’auratan. Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da shirin sun yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan gagarumar gudunmawa da ya bayar a cikin rayuwarsu.
Daga ƙarshe gwamnatin ta tura wa kowace amarya ₦200,000 a matsayin sadaki da kuma kuɗin da za su yi amfani da su domin su ja jari, an kuma gwangwaje kowace amarya da sabbin kayan ɗaki na zamani.
Jagoran shirin Malam Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa, gwamnatin jihar Kano ta ware kimanin Naira Miliyan ɗari uku 300m domin gudanar da wannan auren.