Bayan kammala wasannin cin kofin duniya da aka yi a kasashen Amurka da Mexico da kuma Canada. An samu wani labari da ke bayyana cewa an yi wa shahararren ɗan wasan Argentina, Lionel Messi, barazanar kai masa hari da bama-bamai yayin gasar cin Kofin Duniya ta FIFA da aka gudanar a Amurka da Mexico da kuma Canada.
Jaridar MARCA ta ƙasar Sifaniya, ita ce ta ruwaito cewa wani rahoton ’yan sanda ya bankaɗo wasu shirye-shiryen kai hari a kan Messi, inda wasu mutane suka yi barazanar tayar da bama-bamai tare da kutsawa cikin filayen wasan da yake fafatawa domin ganin sun gama da shi.
Rahoton ya ce Messi ya fuskanci barazana fiye da sauran ’yan wasan da suka halarci gasar, ciki har da wata barazanar kai harin ƙunar baƙin wake kafin wasan zagaye na 16 wanda Argentina ta buga da ƙasar Egypt. Har wa yau, wani mutum ya wallafa a kafar sada zumunta yana barazanar amfani da bama-bamai wajen kai wa Messi hari. Wannan barazana ta sa jami’an tsaro suka gudanar da cikakken bincike a filin wasan Atlanta, Wanda ta sa aka yi amfani da karnukan gano abubuwan fashewa, duba da samun rahotannin cewa an ɓoye bama-bamai a cikin kwandunan shara.
Sai dai har aka kammala binciken, binciken bai samu nasarar gano wani abu mai hatsari ba, inda daga bisani jami’ai suka tabbatar da cewa farfaganda ce kawai.
Jaridar MARCA ta sake ruwaito cewa an samu wata barazana kafin wasan rukuni tsakanin Argentina da Jordan, inda wani mutum ya kira filin jirgin saman Dallas yana cewa shi da wasu mutane biyu za su je filin wasa ɗauke da bama-bamai da bindigar AR-15, tare da bayyana Messi a matsayin wanda suke son kai wa hari. Rahoton ya ƙara da cewa Cristiano Ronaldo ma bai tsira daga irin wadannan barazanar ba, inda aka kama wasu mutane yayin gasar bisa zargin yin barazana ga rayuwarsa.
Hukumomin tsaro, ciki har da FBI, sun yi aiki tare da hukumomin ’yan sanda na ƙasashen duniya wajen bibiya tare da daƙile duk wata barazanar da aka yi wa fitattun ’yan wasan gasar domin ganin babu abin da ya faru gare su.
Haka kuwa aka yi, har aka kammala wasan babu wani abu na alhinin da ya samu ko mutum guda.