"Ba Iya Cire Tallafin Mai Tinubu Kawai Ya Yi Ya, Ya Ƙirƙiro Wata Hanya Ne Domin damka Dukiyar Kasa Ga Abokansa" Atiku

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu da yin almundahana a kan batun cire tallafin man fetur.

Ya bayyana cewa, ba zai yiwu gwamnati ta ce ta kawo ƙarshen tallafin man fetur ba, bayan tana bi ta bayan fage tana bai wa masu zuba jari a harkar man fetur rangwamen haraji, da kuma tallafin kuɗi da sauran gata na musamman ba.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Lahadi, Atiku ya bayyana cewa, batun da gwamnatin Tinubu ke yi kan cire tallafin a matsayin ɗaya daga cikin babbar yaudarar tattalin arziƙi da ya yi wa ’yan Nijeriya.

Ya ce yayin da talakawa ke fuskantar hauhawar farashin man fetur da sufuri da hauhawar farashin kayan abinci, gwamnati na ci gaba da rage wa manyan masu zuba jari a masana’antar man fetur haɗarin kasuwanci ta hanyar ba su rangwamen haraji da sauran tallafe-tallafe.

Har wa yau, ya sake yin nuni da yin bayani a kan asusun NNPC, inda ya ce an kashe kusan Naira tiriliyan 4.84 a shekarar 2023 da kuma Naira tiriliyan 7.13 a shekarar 2024 kan abubuwan da aka bayyana da “energy security” da sauran giɓin farashin man fetur.

A sanarwar Atiku ya tambayi dalilin da ya sa gwamnati ke cewa tallafin man fetur ya ƙare, alhali har yanzu ana amfani da kuɗin gwamnati wajen ɗaukar wasu daga cikin giɓin farashin.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce shirinsa na Atiku Economic Recovery Plan ba ya nufin dawo da tsohon tsarin tallafin man fetur da ya kira mara gaskiya da cike da almundahana ba.

A cewarsa, abin da yake son yi shi ne samar da tallafi mai iyaka, bayyananne kuma za a dinga binciken yadda ake kashe kuɗinsa, tare da ƙara tace ɗanyen mai a cikin gida, tare da inganta gasa da kuma samar da ingantaccen tsarin sufuri.

Atiku ya ce ba na adawa da bai wa masu zuba jari gata, amma ya kamata a yi amfani da irin wannan tsarin wajen rage wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwa.

Har wa yau, Atiku yaa buƙaci gwamnati ta bayyana waɗanda ke cin gajiyar rangwamen haraji da sauran gata da ake bai wa masu zuba jari a masana’antar man fetur, da kuma adadin kuɗin da gwamnati ke rasawa sakamakon hakan.

Ya ce ma’aunin nasarar gyaran tattalin arziƙi bai kamata ya zama yawan wahalar da ’yan ƙasa ke sha ba, sai dai ko rayuwarsu ta inganta, kasuwanci ya bunƙasa, a samar da ayyukan yi, kuma iyalai su iya biyan buƙatunsu na yau da kullum.

Daga ƙarshe Atiku ya sake jaddada cewa zai ci gaba da neman aiwatar da tsarin tallafin da aka yi niyya ga ’yan Nijeriya masu fama da tsadar rayuwa, duk da adawar gwamnatin Tinubu.

Post a Comment

Previous Post Next Post