Sojojin Najeriya Sun Kama Masu Safarar Makamai Uku a Zamfara, Sun Ceto Mutane Shida

Dakarun Brigade ta 1 na Rundunar Sojin Najeriya sun kama wasu mutane uku da ake zargi da safarar makamai, tare da kwato bindigar AK-103-2 guda ɗaya da harsasai 30 a yayin wani samame a Jihar Zamfara.An kama waɗanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 2:05 na rana ranar Lahadi, yayin da sojojin ke gudanar da binciken ababen hawa a kan hanyar Kauran Namoda zuwa Shinkafi. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojojin Brigade ta 1 da ke Gusau, Kyaftin Yusuf Mohammed, ya fitar ranar Litinin.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Lukman Sulaiman mai shekaru 20 da Nafiu Isa mai shekaru 18, waɗanda ake zargin sun fito ne daga Yar-Galadima, gundumar Dan-Sadau, da kuma Adamu Lawali mai shekaru 60, wanda shi ne direban motar.

Rundunar ta ce an gano bindigar AK-103-2, magazine guda ɗaya da harsasai 30 na musamman masu girman 7.62mm, waɗanda aka ɓoye cikin buhun gero a wata motar Golf Wagon mai lambar rajista BMJ-143AA.

An kai waɗanda ake zargin, makamin, harsasan da motar zuwa hannun hukumomi domin ci gaba da gudanar da bincike da kuma ɗaukar matakin doka da ya dace.

Rundunar Sojin ta kuma bayyana cewa tana ci gaba da ƙoƙarin cafke Tijani Goguwa, wanda ake zargin shi ne mamallakin makamin.

A wani samame da aka gudanar a wannan rana, dakarun da aka girke a Forward Operating Base Anka sun ceto mutane shida bayan da wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne suka kai hari kan wata mota a Gadan Manya, da ke kan babbar hanyar Anka zuwa Gummi.

A cewar rundunar, na’urorin sa ido sun gano harin da misalin ƙarfe 2:30 na rana, lamarin da ya sa sojojin gaggauta isa wurin tare da tunkarar maharan yayin da suke ƙoƙarin tilasta fasinjojin motar shiga cikin daji.

Rundunar ta ce shiga tsakani cikin gaggawa da sojojin suka yi ya tarwatsa shirin ’yan ta’addan, inda suka tilasta musu barin mutanen shida tare da tserewa daga yankin.

Daga bisani sojojin sun ceto mutanen shida tare da kwashe su zuwa Babban Asibitin Anka domin kula da lafiyarsu.

Rundunar ta ce uku daga cikin mutanen da aka ceto sun samu ƙananan raunuka a jikinsu, kuma suna karɓar magani a asibitin cikin kwanciyar hankali.

Post a Comment

Previous Post Next Post