Gobara ta tashi a daren Lahadi a shahararriyar kasuwar Oranyan da ke karamar hukumar Bandana Arewa maso Gabas a jihar Oyo, inda ta lalata shaguna da dama tare da asarar dukiyoyi da kayayyaki na miliyoyin naira.
Shagunan da gobarar ta shafa sun hada da na masu sayar da kayan ado na zinariya, kayan daki, kayan sawa na hannu da sauran kayayyaki.
Wata ‘yar kasuwa mai suna Iya Alia ta ce gobarar ta fara ne da tsakar dare, kafin ta bazu zuwa wasu shaguna. Ta ce kusan shaguna 300 ne abin ya shafa.
Sai dai shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, Morof Akinwande, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ba za a iya tantance adadin shagunan da suka kone ba a yanzu.
A cewarsa, gobarar ta fara ne a tsakiyar kasuwar bayan wani abu da ya yi kama da abin fashewa. Ya ce an samu nasarar shawo kan gobarar tun misalin karfe 1 na dare.
Ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin gobarar da kuma tantance adadin shagunan da kayayyakin da suka lalace.
Wannan ba shi ne karon farko da gobara ke lalata kasuwar ba, domin a shekarar 2024 gobara ta kone shaguna sama da 200 a bangaren masu sayar da magungunan gargajiya na kasuwar.
