Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce batun mayar da tallafin man fetur da aka cire ba zai zama wani alkawari da za a yi kawai a lokacin yaƙin neman zaɓe ba.
Yilwatda ya kuma yi Allah-wadai da shawarar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, na mayar da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja, Yilwatda ya bayyana shawarar Atiku a matsayin sauyin matsaya mai matuƙar tayar da hankali, wadda ke haifar da tambayoyi kan shirin ’yan adawa na tafiyar da Najeriya.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa mai ba Yilwatda shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Mista Abimbola Tooki, ne ya fitar da sanarwar.
Yilwatda ya ce al’ummar Najeriya sun cancanci samun cikakken bayani fiye da alkawuran da ake yi a lokacin zaɓe. Ya ƙara da cewa duk wata shawarar dawo da tsarin tallafin da ke kashe makudan kuɗaɗe dole ne a yi mata cikakken nazari, musamman ganin irin nauyin da tallafin ya ɗora wa kuɗaɗen gwamnati da kuma matsalolin da ya haifar a tattalin arziki.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara hedikwatar ƙungiyar City Boy Movement da ke Abuja, inda ya duba cibiyoyin ƙungiyar tare da tattaunawa da shugabanninta.
Shugaban APC ya ce a cikin shekaru uku da suka gabata, an sha ƙalubalantar jam’iyyun adawa da su bayyana wa ’yan Najeriya abin da za su yi daban idan aka ba su damar mulki, amma har yanzu ba a fito da wani cikakken tsari mai ma’ana da gamsarwa ba.
Yilwatda ya ce abin tambaya ne yadda Atiku, bayan shafe sama da shekaru uku ba tare da gabatar da cikakken shirin tafiyar da ƙasa ba, ya fito yanzu, kusan watanni huɗu kafin babban zaɓen 2027, da wata manufa da za ta iya mayar da wasu daga cikin sauye-sauyen tattalin arzikin da aka samu.
A cewarsa, shawarar Atiku za ta iya mayar da Najeriya baya da shekaru da dama ta fuskar ci gaba.
Yilwatda ya ce bai kamata a mayar da manufofin tattalin arziki zuwa alkawuran lokacin zaɓe kawai ba. Ya ce ya kamata ’yan Najeriya su san daga ina za a samo kuɗin aiwatar da irin wannan manufa, waɗanne ɓangarorin tattalin arziki za su ɗauki nauyin kuɗin, da kuma ko za a iya dorewar tsarin ba tare da sake jefa ƙasar cikin matsalolin kuɗaɗen gwamnati da suka tilasta yin garambawul ba.
Shugaban APC ya jaddada cewa cire tallafin man fetur wani mataki ne mai wahala, amma wajibi ne domin gyara tattalin arzikin ƙasar. Ya ce sakamakon matakin na buƙatar wasu ƙarin manufofi da za su rage wa jama’a raɗaɗin cire tallafin, faɗaɗa shirye-shiryen tallafa wa al’umma, da kuma ƙarfafa ɓangarorin da ke samar da arzikin ƙasa.
Ya ƙara da cewa ainihin gwajin shugabanci ba shi ne iya yin alkawarin kawo sauƙi cikin gaggawa domin samun ribar siyasa a lokacin zaɓe ba, sai dai ƙarfin guiwar ɗaukar matakai masu wahala domin amfanin ƙasa na dogon lokaci.