"Ba Za Mu Lamunci Yawon Da Manyan Motoci Ke Yi a Cikin Birni Da Rana Kata Ba"

Gwamnatin Kano za ta haramta zirga-zirgar manyan motoci a cikin ƙwaryar birnin Kano da rana.

Gwamnatin Jihar ta Kano ta sanar da shirin taƙaita shigowar manyan motoci cikin ƙwaryar birnin Kano daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na dare, domin rage cunkoson ababen hawa da inganta zirga-zirga.

Kwamishinan sufuri na jihar, Hon. Haruna Isa Dederi, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce an kammala shirye-shiryen fara aiwatar da sabuwar dokar.

Kwamishina ya ce matakin ya zama dole ne sakamakon ƙaruwa da yawan jama’a a jihar da kuma kasancewar Kano babbar cibiyar kasuwanci a yankin.

Dederi ya bayyana cewa shirin yana daga cikin wani ɓangare na haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da wani kamfani mai zaman kansa domin zamanantar da tsarin kula da zirga-zirgar ababen hawa da inganta harkokin sufuri.

A cewarsa, hanyoyin shiga birnin guda shida ne, kuma za su kasance ƙarƙashin sabon tsarin. Su ne hanyoyin da suka haɗa daga: Kano zuwa Katsina, da Kano zuwa Zariya da Kano zuwa Ɗanbatta da Kano zuwa Gwarzo da kuma Kano zuwa Wudil da Hadejia.

Ya ƙara da cewa, taƙaita shigowar manyan motocin zai taimaka wajen rage cunkoso a manyan hanyoyin shiga birnin tare da sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da harkokin kasuwanci.

Shi ma Manajan Daraktan kamfanin da ke haɗin gwiwa da gwamnatin jihar, Kafilu Abdulƙadir, ya ce irin wannan tsari da aka fara amfani da shi a Jihar Legas a shekarar 2007 ya taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa ta hanyar samar da wuraren ajiye manyan motoci.

Abdulkadir ya bayyana cewa za a gina babbar tashar ajiye manyan motoci a Daka Tsalle, yana mai cewa sama da manyan motoci 3,000 ne ke shiga Kano a kullum.

Ya ƙara da cewa tashar na daga cikin matakan da ake ɗauka domin rage cunkoson ababen hawa a manyan hanyoyin shiga birnin Kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post