"IBB Ya Taba Gargadar Obasanjo Akan Atiku Abubakar" In Ji Duke

Ibrahim Badamasi Babangida ya taɓa gargaɗin Obasanjo kan Atiku in ji Donald Duke

A cikin wata saɗara, tsohon gwamnan Jihar Cross River, Donald Duke, ya bayyana cewa tsohon shugaban mulkin soja, Janaral Ibrahim Babangida (IBB), ya taɓa gargaɗin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo da kada ya yarda da mataimakinsa Atiku Abubakar a wancan lokacin.

Duke ya bayyana haka a cikin sabon littafin Seun Oloketuyi mai suna How to Win Elections in Nigeria, wanda ya yi bayani kan siyasar Nijeriya a farkon jamhuriya ta huɗu.

A cewar Duke, yayin da Obasanjo ke shirin neman wa’adi na biyu a shekarar 2003, dangantakarsa da Atiku ta fara yin tsami, lamarin da ya haifar da shakku kan goyon bayan Atiku ga sake zaɓen shugaban.

Duke ya ce wasu gwamnoni 10 sun gana da shugaban PDP na lokacin, Solomon Lar, domin tattauna yiwuwar sauya ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa. Obasanjo ya kira shi da daddare yana ƙorafin abin da ya kira cin amana daga mataimakinsa, inda Duke ya roƙe shi da ya kwantar da hankali. Daga bisani, Atiku ya shirya ganawar Obasanjo da Babangida da tsohon shugaban ƙasa Abdulsalami Abubakar a fadar shugaban ƙasa.

Duke ya ce bayan ganawar, yayin da Babangida da Obasanjo suka koma ɗakin Obasanjo su kaɗai, IBB ya tunatar da shi cewa ya taɓa gargaɗinsa kada ya yarda da mataimakinsa. A cewar Duke, Babangida ya kalli Atiku bayan sun dawo wurin sauran mutanen, sannan ya ce wa Obasanjo: “Wannan ba zai iya mulkin Nijeriya ba.”

Duke ya ce abin da ya faru ya nuna irin tsananin rashin amincewar da ke tsakanin Obasanjo da Atiku a wancan lokaci. Rikicin siyasar mutanen biyu ya sake kunno kai a baya-bayan nan, bayan Obasanjo ya zargi Atiku da bayar da Naira miliyan 5 ga marigayi Ghali Umar Na Abba domin fara yunƙurin tsige shi a wa’adinsa na farko.

Sai dai, Atiku ya musanta zargin, tare da cewa Obasanjo na ƙirƙirar zarge-zargen ne saboda ya nuna adawa da shirin Atiku na neman takar shugabancin ƙasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post