Kwana ɗaya bayan ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen 2027, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce zai dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban Nijeriya a zaɓen 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a jiya Laraba, inda ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta gaza bayyana yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur.
Ya ƙara da cewa bai yi adawa da cire tallafin ba tun farko, amma ya nemi gwamnati ta bayyana inda kuɗaɗen suka tafi, musamman ganin cewa an ce za a yi amfani da su wajen rage talauci da taimaka wa yara wajen samun ilimi.
Ɗan takarar na ADC ya ce idan ya samu nasarar lashe zaɓen na 2027, zai dawo da tallafin man fetur, tare da tabbatar da cewa duk wanda ya yi amfani da kuɗaɗen ba bisa ka’ida ba ya mayar da su.
Ya ƙara da cewa, cire tallafin zai iya zama abin fahimta idan da an karkatar da kuɗaɗen da aka samu zuwa ayyukan raya ƙasa da inganta tsaro da ilimi da kuma samar da damammaki ga matasa.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya sanar da cire tallafin man fetur a jawabinsa na rantsarwa a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Matakin da ya haifar da tashin farashin man fetur, wanda ya kuma janyo tsadar kayayyaki da sauran abubuwan more rayuwa a faɗin ƙasar. Sai dai wasu gwamnonin jihohi sun bayyana cewa rabon kuɗaɗen da suke samu daga Asusun Tarayya (FAAC) ya ƙaru sosai tun bayan cire tallafin.
A ranar Laraba, Ministan Kuɗi kuma Ministan da ke kula da tattalin arziƙi, Taiwo Oyedele, ya ce cire tallafin man fetur ya samar da albarkatun kuɗi har naira tiriliyan 15.8 ga tarayya tsakanin watan Yunin 2023 da Disamban 2025. Oyedele ya ƙara da cewa kuɗaɗen sun samu ne ta hanyar ƙarin kuɗaɗen shiga, musamman sakamakon sauyin darajar naira a kan hada-hadar da ake yi da dala bayan garambawul kan tsarin canjin kuɗi.