Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sanarwar naɗin Abel Olumuyiwa Enitan a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayyar Nijeriya (HCSF), wanda zai fara aiki daga ranar Laraba 27 ga Agusta, 2026.
Mai girma Enitan zai maye gurbin Didi Esther Walson-Jack, wadda za ta yi ritaya bayan ta kai shekarun ritaya na doka, wato shekaru 60 cifcif
A halin yanzu, Enitan shi ne Sakataren Dindindin mafi girma a cikin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, wanda ya shafe shekaru bakwai (7) da watanni 7 yana riƙe da muƙamin Sakataren Dindindin. A tsawon wannan lokaci, ya yi aiki a Ma’aikatar Harkokin ’Yan Sanda da Ma’aikatar Harkokin Jin Ƙai, da Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa. A yanzu yana matsayin Sakataren Dindindin na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.
Shugaba Tinubu ya yaba wa Didi Walson-Jack bisa gudummawarta wajen sauye-sauye da ƙirƙire-ƙirƙire da ta kawo tare da yadda ta inganta tsarin aikin gwamnati a lokacin da take jagorantar ma’aikatar gwamnatin tarayya.
Har wa yau, Shugaba Tinubu ya umurci sabon Shugaban Ma’aikatan da ya ƙarfafa sauye-sauyen da ake yi, tare da inganta ƙwarewa da ingancin aiki, da kuma tabbatar da cewa ma’aikatan gwamnati suna aiki bisa ƙwarewa da cancanta da gaskiya da riƙon amana da kuma kishin hidimar jama’a.
Abel Olumuyiwa Enitan, wanda ya fito daga Jihar Osun, zai fara jagorantar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya a hukumance daga ranar Laraba 27 ga Agustan 2026.