Darakta Janar na harkokin yaɗa labaran Gidan Gwamnatin Gombe, Isma'ila Uba Musulmi ya bayyana wani saƙo a shafinsa inda yake bayyana aniyar Gwamnatin jihar Gombe a kan nasarar da 'yarsu Maryam Ibrahim Ɗan'azumi.
Hadimin ya bayyana cewa: Gwamna Inuwa Yahaya ya taya Hafiza Maryam Ɗan’azumi murna, yayin da ta zama zakara ta farko a gasar Alƙur’ani ta ƙasa da ƙasa a da aka gudanar a ƙasar Saudiyya
Gwamnan yana sa ran karrama zakarar da kansa bayan Allah ya yi mata dawowa. Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya bayyana matuƙar farin ciki da alfahari bisa gagarumar nasarar da wata ‘yar jihar Gombe, Maryam Ibrahim Ɗan’azumi, ta samu a matakin ƙasa da ƙasa, inda ta zama zakara ta farko gabaɗaya a gasar Alƙur’ani ta ƙasa da ƙasa ta Sarki Abdulaziz karo na 46, da aka gudanar a Masarautar Saudiyya.
Maryam, wadda take karatu a Abubakar Siddiq Community Islamic School for Qur’anic Memorisation, da ke Herwagana Quarters, Gombe, ta wakilci Nijeriya a wannan gasa mai matuƙar daraja. Ta fafata a rukunin haddar Alƙur’ani Mai Girma gaba ɗaya, karatu, Tajweed da kuma tafsiri (Hizb 60 tare da Tafsiri) inda ta samu nasara tazo ta farko a cikin dukkan mahalarta gasar daga ƙasashe daban-daban. Maryam wadda ta nuna ƙwarewa ta musamman, haƙiƙa ta sanya Gombe da Nijeriya sun samu karɓuwa da yabo a duniya. Wannan nasara ta kasance mai matuƙar muhimmanci saboda ita ce karo na farko da mata suka shiga gasar a cikin tarihin gasar na shekaru 46. Saboda haka, nasarar Maryam ta zama babbar abar tunawa a tarihi kuma abar alfahari.
Gwamna Yahaya, a cikin wata sanarwa da ya fitar domin murnar wannan gagarumar nasara, ya taya Maryam da iyalanta da malamanta da ɗaukacin al’ummar Musulmin Gombe murna. Ya bayyana nasarar tata a matsayin babban abin alfahari ga Jihar Gombe da Nijeriya bakiɗaya.
Gwamnan ya ce nasarar Maryam tana nuna muhimmancin ladabi, jajircewa da himma wajen neman ilimi, yana mai cewa nasarar da ta samu a matakin duniya ta nuna irin hazaƙa da damar da matasan Jihar Gombe suke da ita.
Ya ƙara da cewa: “Ina matuƙar alfahari da gagarumar nasarar da ‘yarmu ta samu a fagen duniya. Nasarar Maryam ta nuna ƙwarewa da kuma kyakkyawar al’adar ilimi da Gombe ta gada. Nasararta ta kawo alfahari ba ga Gombe kaɗai ba, har ma da Najeriya bakiɗaya. Ina da yaƙinin cewa wannan nasara za ta ƙarfafa matasa da dama, musamman ‘yan mata, su nemi ƙwarewa kuma su yi fice a fannonin da suka zaɓa.”
Gwamnan ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatinsa na tallafawa ci gaban ilimin matasa, ciki har da karatun Alƙur’ani da sauran ilimin addini, wanda ya bayyana cewa yana da muhimmiyar rawa wajen tarbiyyar ladabi, kyawawan halaye da zama ɗan ƙasa nagari.
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da nuna goyon baya tare da karrama mutanen da nasarorinsu ke tallata kyakkyawan sunan Jihar Gombe a cikin Nijeriya da kuma ƙasashen duniya.
Gwamna Yahaya ya ce: “Ƙudurimmu na inganta tafiyar ilimin matasa, musamman a fannin karatun addini, ba zai girgiza ba. Mun fahimci irin rawar da ilimin addini ke takawa wajen gina ɗabi’a da kuma taimakawa wajen ci gaban al’umma.
An san Gombe da ƙwarewa, kuma za mu ci gaba da tallafawa waɗanda suke inganta kyakkyawan sunan Gombe a duniya. Maryam tana cikin irin waɗannan mutane, kuma muna alfahari da yin murnar nasararta.”
Gwamnan ya bayyana cewa nasarar Maryam ta fi zama abin mamaki saboda yadda ta fara daga matakin ƙaramar hukuma, ta wuce zuwa matakin jiha, sannan ta zama ta farko a matakin ƙasa, kafin daga ƙarshe ta wakilci Nijeriya a gasar ƙasa da ƙasa da aka gudanar a Makkah, Saudiyya.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce yana sa ran karɓar Maryam da kansa tare da karrama ta bayan dawowarta Nijeriya. Ya bayyana cewa irin wannan karramawa za ta ƙarfafa ta ta ci gaba da neman ƙwarewa, sannan ta zama abin ƙarfafa gwiwa ga sauran matasa su yi burin samun irin wannan matsayi.
Gwamnan ya yi kira ga iyaye da malamai da cibiyoyin addini da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da tallafa wa matasa masu hazaƙa, musamman ta hanyar samar musu da goyon baya da damar da za su taimaka musu wajen haɓaka basirarsu da kuma bayar da gudummawa mai amfani ga al’umma.
Gwamnan ya kuma yaba da rawar da Abubakar Siddiq Community Islamic School for Qur’anic Memorisation ta taka, yana mai cewa makarantar ta bayar da gagarumar gudummawa wajen haɓaka hazakar wannan matashiya mai nasara.
Abin ban sha’awa shi ne, Gwamna Inuwa Yahaya da kansa shi ne Shugaban farko na Hukumar Gudanarwar makarantar, kafin ya zama Gwamna. Bayan ya hau kujerar gwamna, sai ya bar wannan matsayi ga Architect Yunusa Yakubu.
Saboda haka, alaƙar Gwamnan da wannan makaranta ta ƙara wani muhimmin ɓangare ga wannan gagarumar nasarar Maryam, tare da nuna irin dogon lokaci da Gwamnan yake ba da muhimmanci ga ci gaban matasa a Jihar Gombe.