Cutar Mashako Ta Kashe Yara Kimanin 50 a Kano

Rahotanni sun ce cutar mashako wato Diptheria ta kashe mutane kimanin 50, akasarinsu yara, a karamar hukumar Rano ta Jihar Kano.

Yara

Lamarin ya sa wani dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Rano, Ibrahim Muhammad, ya gabatar da kudirin gaggawa a zaman majalisar ranar Talata, inda ya bukaci gwamnati ta dauki matakan dakile yaduwar cutar.

Dan majalisar ya ce cutar ta fi kamari a garuruwan Ridin da Sabuwar Qaura, inda aka samu mace-macen yara da kuma wasu da aka kwantar a asibitoci.

Ya bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf da Ma’aikatar Lafiya su kara tallafin gaggawa, ciki har da magunguna da tura ma’aikatan lafiya zuwa yankunan da abin ya shafa.

Wani dan majalisar, Usman Abubakar Tasiu, ya ce cutar ta kuma yadu zuwa wasu yankunan karamar hukumar Kiru, ciki har da Kwanar Dangora, Dangora da Yelwa. Ya bukaci kafa kwamitin gaggawa domin daidaita yaki da cutar a Rano, Tudun Wada, Kibiya, Bunkure, Bebeji da Kiru.

Haka kuma, Saleh Ahmad ya bukaci gwamnati ta kara kaimi wajen yin allurar rigakafi da sauran matakan kariya, yayin da Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Lawan Husseini, ya nemi a yi amfani da dokar kare lafiyar jihar wajen dakile barkewar cutar.

Majalisar ta amince da kudirin tare da umartar Kwamitin Lafiya da ya tuntubi Ma’aikatar Lafiya kan matakan aiwatar da dokar da kuma samar da agajin gaggawa ga al’ummomin da abin ya shafa.

Post a Comment

Previous Post Next Post