Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci rundunar soji, ’yan sanda, DSS da sauran hukumomin tsaro da leƙen asiri da su ƙaddamar da aikin ceto gomman mutanen da aka sace a wani hari a jihar Neja da ke tsakiyar ƙasar.A wata sanarwa da shugaban ya fitar, ya bayyana takaicinsa kan sacewa da kashe wasu fararen hula da miyagu suka yi a jihar, inda ya ce waɗanda suka kai harin ba za su tsere wa hukunci ba.
“Waɗanda suka kai wannan mummunan hari kan ƴan Najeriya, maƙiyan zaman lafiya ne kuma maƙiyan bil’adama ne, kuma ba za su tsira daga hukunci ba," in ji Tinubu.
Tinubu ya ce gwamnati ba za ta huta ba har sai an dawo da ƴaƴa, iyaye da sauran mutanen da aka sace ga iyalansu lafiya.
Ya kuma umarci shugabannin hukumomin tsaro da su riƙa ba shi rahoto kan ci gaban aikin ceto har sai an gano duk mutanen da aka sace.
Tinubu ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya za ta ba gwamnatin jihar Neja dukkan goyon bayan da ake buƙata domin aikin ceto mutanen.