Dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa Ta OPERATION FANSAN YAMMA Sun Kama Wasu Kayan Fashewa Guda 180 a Jihar Zamfara a Kan Hanyarsu Ta Zuwa Katsina

Rundunar sojojin ƙasa, sun kama kayan fashewa ɗari da tamanin (180) waɗanda za a kai wa 'yan bindiga a jihar Katsina.

Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta OPERATION FANSAN YAMMA sun kama wani mutum da ake zargi da safarar makamai, haɗi da ƙwace wasu kayan fashewa guda 180 a jihar Zamfara, yayin da suke ƙoƙarin tsallakawa zuwa jihar Katsina.

Kakakin rundunar, Laftanal Kanal Aliyu Ɗanja, ya ce an kama wani mutum wanda yake tafe da kayan mai shekaru 57 mai suna Sani Umar a jiya Juma’a 14/08/2026, yayin da sojoji ke gudanar da binciken ababen hawa a kan hanya.

Jami'in ya ci gaba da cewa, binciken motar da mutumin yake a ciki, shi ne ya kai mu ga bankaɗo wasan kayan fashewa guda 180, nau’in 20mm Super Power da suke ƙudundune a cikin motar.

A cewar rundunar, ana zargin cewa kayan fashewar sun fito ne daga ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara, domin kai su ga wasu ’yan ta’adda da ke aiki a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

A halin yanzu, Sani Umar wanda aka kama ɗauke da kahan haɗi da motarsa da kuma kayan fashewar da aka ƙwato duka suna hannun jami’an tsaro domin ci gaba da gudanar da ƙarin bincike.

Post a Comment

Previous Post Next Post