Wasu rahotanni daga jihar Osun sun bayyana cewa, rundunar ‘yansandan Jihar ta Osun ta kama wani jami’inta da aka ɗauka a bidiyo yana sakin hayaki mai sa hawaye a yayin zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar da safiyar yau Asabar.
An bayyana cewa, lamarin ya faru ne a cibiyar tattara jami’an zaɓe, da ke Ward 10 a Modakeke, da ke ƙaramar hukumar Ife East, ba a rumfar zaɓe ba kamar yadda wasu bayanai ke yawo a kafafen sada zumunta.
An gani a wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, wani jami’in ‘yan sanda ya harba barkonon tsohuwa, yayin da wani mai magana da harshen Yarbanci ke zargin cewa jami’an ‘yansandan ne suka harba hayaƙin kan masu kaɗa ƙuri’a ba tare da wani dalili ba.
A lokacin da take martani a kan lamarin, rundunar ‘yansandan jihar Osun ta ce jami’in da abin ya shafa na daga cikin jami’an da aka tura cibiyar, kuma sakin hayaƙin ya faru ne ba da gayya ba.
Rundunar ta ce: “Hankalin Rundunar ‘yansandan Jihar Osun ya karkata ga rahotanni da bidiyoyin da ke yawo a kafafen sada zumunta kan wani lamari da ake zargin ya faru a Ward 10, Modakeke, da ke ƙaramar hukumar Ife East, inda wani jami’in da aka tura cibiyar RAC ya harba barkonon tsohuwa ba da gangan ba.”
‘Yansandan sun bayyana cewa jami’in yana ƙoƙarin sauke nauyin kansa ne lokacin da lamarin ya faru, inda suka bayyana halinsa a matsayin “abin Allah wadai sosai”, tare da cewa hakan bai dace da ƙa’idojin da ake tsammanin jami’an rundunar ‘yansandan Nijeriya da bi ba.
Daga ƙarshe rundunar ta bayyana cewa an kama jami’in domin gudanar da bincike a kan abin da ya faru.