Dan Takarar Shugaban Kasa A Nijeriya Atiku Abubakar Ya Koka Kan Shigar Kudi Cikin Asusun Bakinsa Ba Tare Da Saninsa Ba

Tsohon mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwa kan wasu kudade da aka tura cikin ɗaya daga cikin asusunsa na sirri ba tare da saninsa ko amincewarsa ba.

Atiku Abubakar

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Juma'a, an ce wani mutum da ba a san ko wanene ba ne ya tura kuɗin tare da rubuta cewa: "Contribution Electioneering Campaign."

Atiku ya ce ba shi ko tawagarsa suka nemi ko suka amince da wannan kuɗi ba, yana mai cewa abin ya tayar da tambayoyi kan yadda aka samu bayanan asusun nasa na sirri, wanda ba a bayyana wa jama'a ba.

Ya kuma bayyana cewa idan har bayanan sirrin asusun tsohon mataimakin shugaban ƙasa za su iya shiga hannun wasu ba tare da izini ba, hakan na nuna cewa sirrin kuɗaɗen 'yan Najeriya na cikin haɗari.

Atiku ya yi zargin cewa wataƙila wasu masu damar samun bayanan sirri ne suka fitar da su, yana mai gargadin cewa hakan na iya jefa masu asusun cikin haɗarin masu garkuwa da mutane, 'yan ta'adda, 'yan bindiga da masu damfara.

Ya ce an sanar da hukumomin tsaro da kuma al'umma game da lamarin, yana mai bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da ke tayar da hankali gabanin zaɓen 2027. Haka kuma ya buƙaci 'yan Najeriya da kada su bari irin waɗannan abubuwa su karkatar da hankalinsu daga manufofinsa na siyasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post