Jami'an Hukumar Hana Fasa Ƙwauri (Kwastam) ta Najeriya (NCS) ta bayyana cewa ta samu nasarar damƙe wasu bindigogi ƙirar (pump-action) guda ɗari da arba'in (140) da kuma kayan abinci waɗanda aka gauraye su da tabar wiwi waɗanda darajarsu ta kai Naira miliyan 373.8 a Tashar Jiragen Ruwa ta TinCan da ke Legas.
Babban jami'in, Kwanturolan hukumar Kwastam, Bashir Adeniyi ne ya bayyana cewa, an gano sassan bindigogin ne a cikin wata kwantena da aka ɓoye su a ciki, ya zuwa yanzu dai an riga da an haɗa bindigu 140 daga cikinsu, kuma ana ci gaba da haɗa sauran sassan.
Jami'in ya ci gaba cewa, bayan faruwar abin, an kama manyan mutane guda biyu waɗanda ake ƙarfafa zargi a kansu, yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da farautar wani da ake nema ruwa a jallo.
Adeniyi ya ce jami'an kwastam sun kama manyan motocin kwantena guda biyu waɗanda suke ɗauke da biskit da alewa da sauran kayan ciye-ciye waɗanda aka gauraye su da tabar wiwi, waɗanda aka ɓoye su a cikin motocin da aka shigo da su. Har wa yau a cikin motocin akwai: janareto da batura da kuma yadudduka.
Sai dai babban jami'in ya tabbatar da cewa lallai an shirya kayan ne cikin salo mai kama da kayan ciye-ciye na yau da kullum domin ɗauke hankalin yara da matasa, wanda hakan yana iya sa mutane su ci kayan ba tare da sun fahimci abin da suka ci, suna ɗauke da miyagun ƙwayoyi ba. Ya ci gaba da cewa: Hukumar NDLEA ta karɓi kayayyakin da aka kama tare da bayyana cewa irin waɗannan kayan na zama sabuwa kuma babbar barazana ga lafiyar al'umma. Hukumar kuma, ta yi kira ga iyaye da makarantu da su ƙara sanya ido kan irin waɗannan kayayyaki sosai.