DG na NYSC Ya Gargadi Matasa Kan Tsoma Baki Cikin Siyasar 2027

Babban Daraktan Hukumar Kula da Masu Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC), Birgediya Janar Nafi’u Olakunle, ya buƙaci mambobin hukumar da su kasance masu tsaka-tsaki, ba tare da shiga harkokin siyasa ba, yayin da yakin neman zaɓen babban zaɓen 2027 ke ƙara faraɗaɗa a faɗin ƙasar.Daraktan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, lokacin da ya ziyarci mambobin Batch ‘B’ Stream II na shekarar 2026 da aka tura Jihar Jigawa, waɗanda ke gudanar da kwas ɗin horaswa na tilas na tsawon makonni uku a sansanin horas da NYSC na dindindin na Yakubu Gowon da ke Fanisau, Dutse.

Wannan gargadi ya zo ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi a sassa daban-daban na ƙasar, bayan da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ɗage haramcin fara yakin neman zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa na 2027.

Da yake jawabi ga mambobin NYSC a sansanin, Olakunle ya ce an kafa shirin NYSC ne domin zama wata hanya ta haɗa kan ‘yan Najeriya, don haka bai kamata wani ɗan ƙungiyar ya mayar da shi wajen gudanar da siyasar jam’iyya ba.

Ya ce: “Dole ne ku kasance masu tsaka-tsaki kuma ku nisanci siyasa a kowane lokaci. Kada ku bari a yi amfani da ku a matsayin ‘yan daba ko wakilan wani ɗan siyasa ko jam’iyyar siyasa. Amincinku yana ga Najeriya ne, ba ga wata jam’iyya ba.”

Daraktan ya kuma yi gargadin cewa duk wani ɗan NYSC da aka samu yana shiga siyasar jam’iyya, yin wa wani ɗan takara kamfen ko wallafa saƙonnin siyasa a kafafen sada zumunta, zai fuskanci tsauraran matakan ladabtarwa bisa tanadin dokokin NYSC.

Ya tunatar da su cewa manufar shirin NYSC ta samar da haɗin kan ƙasa da haɗa kan al’umma ba za ta samu nasara ba face mambobin hukumar sun mutunta dokoki da ƙa’idoji, tare da cika rantsuwar mubaya’ar da suka yi wa ƙasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post