Tinubu Ya Gana da Shugaban ICPC a Fadar Shugaban Kasa

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, Dr Musa Aliyu, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Tinubu

Musa Aliyu ya isa fadar ne da misalin ƙarfe 5:40 na yamma domin ganawar, sai dai ba a bayyana ajandar tattaunawar ba.

Ganawar ta zo kwana guda bayan Tinubu ya umarci ICPC da gudanar da cikakken bincike kan badakalar wata hukumar bogi mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC).

A ranar 6 ga Agusta, Aliyu ya gabatar wa Tinubu da rahoton wucin gadi kan binciken, inda ICPC ta gano cewa PFIPC ba wata hukuma ce da aka kafa bisa doka ko wata sahihiyar umarnin gwamnati ba.

Hukumar ta kuma ce mutumin da ke ikirarin kafa hukumar, Adeniyi Matthew Adeyemi, ya yi amfani da takardun bogi wajen gudanar da ayyukansa tare da ƙirƙirar wasu hukumomi na bogi.

Post a Comment

Previous Post Next Post