Gwamnatin Jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ta ƙaddamar da rabon buhunan hatsi 90,000 ga masu buƙata a faɗin ƙananan hukumomi 34 na jihar.
An tsara wannan tallafi ne domin rage wa al’umma raɗaɗin matsin tattalin arziki da kuma ƙarfafa samar da isasshen abinci, musamman ga zawarawa, tsofaffi, masu buƙata ta musamman da kuma iyalan da ke cikin matsanancin tattalin arziki.
A wajen ƙaddamar da shirin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kaita, Engr. Bello Lawal Yandaki, ya gabatar da jawabin maraba, inda ya bayyana godiya ga Gwamna Radda bisa wannan gagarumin tallafi da ya ce zai taimaka matuka wajen rage wa iyalan da ke fama da ƙalubalen tattalin arziki radadin ƙarancin abinci.
A nata jawabin, Kwamishiniyar Ayyuka na Musamman, Hajiya Zainab Musa Musawa, ta jaddada cewa rabon hatsi wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin jihar na tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi da tabbatar da cewa babu wani ɓangare na al’umma da aka bari a baya. Ta kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa an gudanar da rabon cikin gaskiya da adalci.
Shugaban Shirin Cigaban Al’umma (CDP), Dr. Kamaladdeen Kabir, ya bayyana yadda aka tsara tsarin rabon ta hannun Kwamitocin Matakin Ward (CLCs), domin tabbatar da cewa tallafin ya isa ga waɗanda suka cancanta a matakin al’umma.
A nasa saƙon fatan alheri, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Dr. Bishir Gambo Saulawa, ya yabawa Gwamna Radda kan yadda gwamnatinsa ke aiwatar da shirye-shiryen tallafa wa al’umma, musamman masu buƙata. Ya bayyana rabon hatsi a matsayin wata muhimmiyar shaida ta kishin al’umma da jajircewar gwamnati wajen inganta rayuwar jama’a.
Haka kuma, Sarkin Sullubawan Katsina, Hakimin Kaita, ya bayyana godiya ga gwamnatin jihar bisa wannan tallafi, tare da yabawa yadda aka haɗa shugabannin gargajiya, malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da nasarar shirin.
Gwamna Radda ya umurci dukkan jami’ai da masu ruwa da tsaki da ke da hannu a rabon da su tabbatar da gaskiya, adalci, gaskiya da rikon amana, tare da tabbatar da cewa hatsi ya isa ga waɗanda suka cancanta ba tare da nuna wariya ko fifita wani ba.
Zaa gudanar da rabon ne ta hannun Kwamitocin Matakin Al’umma (CLCs) ƙarƙashin Shirin Cigaban Al’umma na CDP tare da haɗin gwiwar sarakunan gargajiya, malaman addini, hukumomin ƙananan hukumomi da jami’an tsaro.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan tallafi wani ɓangare ne na babbar manufar gwamnatinsa na kawo cigaba ta hanyar taimakon al’umma. Matakan sun haɗa da samar da takin zamani da sauran kayan noma a farashi mai sauƙi, samar da famfunan ban-ruwa, haƙa rijiyoyin burtsatse da kuma wasu shirye-shiryen da za su ƙara yawan amfanin gona tare da rage tsadar abinci.
Wannan sabon tallafi ya ginu ne a kan wasu shirye-shiryen tallafawa al’umma da gwamnatin ta aiwatar a baya, ciki har da tallafawa zawarawa 7,220, rabon kayan abinci da tallafin kuɗi ga ƙananan ‘yan kasuwa a faɗin gundumomi 361 na jihar a watan Ramadan, da kuma rabon kayan abinci tare da haɗin gwiwar Gidauniyar Aliko Dangote.
Mahalarta taron sun hada da mataimakin gwamnan jihar Katsina, Malam Farouq Lawal Jobe, kwamishinoni, jami’an gwamnati, sarakunan galgajiya, da sauran masu ruwa da tsaki.
MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government
August 19, 2026.
