Shari'ar maita a Salem: A Salem, lardin Massachusetts Bay na kasar Amurka, an kashe mutane biyar, mace daya da maza hudu, ciki har da wani limami, bayan an same su da laifin maita.
A Rana Mai Kamar Ta Yau 19 Ga Watan Augusta 1692 akayi shari’ar maita ta Salem: A Salem, lardin Massachusetts Bay, an kashe mutane biyar, mace daya da maza hudu, ciki har da wani limami, bayan an same su da laifin maita.
Shari'ar mayu ta Salem ta kasance jerin shari'o'i da kuma gurfanar da mutanen da ake zargi da maita a Massachusetts a kasar Amurka tsakanin Fabrairu 1692 da Mayu 1693. An zargi fiye da mutane dari biyu. An samu mutane 30 da laifi, goma sha tara daga cikinsu an kashe su ta hanyar rataya (mata goma sha hudu da maza biyar). Wani mutum mai suna Giles Corey, an yi masa Dukan tsiya har lahira, kuma akalla mutane biyar sun mutu a gidan yari.
