Saƙon godiya da ɗan wasan Jamal Musiala na ƙungiyar Bayern Munich ɗan ƙasar Germany ya wallafa a shafinsa, bayan da ya sake faɗuwa a wasansu da ƙungiyar Heidenheim mintina takwas da fara wasan, bayan da a baya ma ya faɗi ana tsaka da wasan sada zumunta da ƙungiyar Leipzig. Ga dai abin da ya ce a takardar da ya wallafa a shafinsa na Facebook .
Labari mafi muhimmanci a farko shi ne, Ina cikin ƙoshin lafiya.
Ina matuƙar godiya da saƙonninku da kuma goyon bayanku a gare ni! Ina fahimtar cewa da yawa daga cikinku kuna cikin damuwa. Wadda nike so in cire muku wannan fargabar a yau kuma in yi muku ɗan bayani:
Na ɗan fuskanci matsalar mantuwa ko rashin kasancewa a hankalina na ɗan lokaci kaɗan wanda nake fatan za a iya magance matsalar, kuma hakan yana da alaƙa da matsalar tsarin jijiya (neurological dysfunction).
Waɗannan na iya kasancewa ɗaya daga cikin lokutan da suka wuce kwanan nan, kamar wasan da muka yi da Leipzig ko kuma yanzu a Heidenheim.
Na san cewa waɗannan abubuwan na iya zama abin tsoro, musamman ga waɗanda suka fara gani a karon farko amma a gare ni, a halin yanzu wannan wani ɓangare ne na rayuwata ta yau da kullum. A yanzu haka ina samun mafi kyawun jiyya daga likitoci kuma ina da ƙwarin gwiwa sosai. Kulob ɗin FC Bayern da na kusa da ni suna tare da ni a kowane lokaci kuma suna goyon baya na a kan wannan turba.
Abin da ke da muhimmanci shi ne babu wani hatsarin lafiya na daban. Ina samun Cikakken haɗin gwiwa da kuma tattaunawa akai akai tare da masana, yana daga cikin burina in fuskanci wannan ƙalubale, kuma tare da amincewar ƙwararru a harkar jijiya in ci gaba da abin da yake zai taimaka mini wajen samun sauƙi sosaĩ: ta hanyar yib rayuwata ta yau da kullum da kuma ci gaba da buga ƙwallon ƙafa da dukkan abubuwan sha'awa ta. Domin wannan na ci gaba da ɗaukaf nauyin kaina. Ina cikin kyakkyawan yanayi gabaɗayana kuma ina jin ina kan hanya madaidaiciya.
Abin da yake fiye da komai taimakona a kan wannan turba shi ne ci gaba da yin nasara da lashe kofuna tare da ƙungiyata da kuma babban goyon bayanku.
Ina fatan za ku fi fahimta ta da kyau. A lokaci guda, ina neman fahimtarku cewa ina son in tsare wannan batu tsakanina da mutanena na kusa, ƙungiyar kulob ɗina, da kuma masana.
Godiya mai tarin yawa,
Naku, J