Tsohon Dan Wasan Real Madrid Roberto Carlos Ya Furta Kalmar Shahada Gaban Wani Malami a Brazil

Mun samu labari daga wasu kafafen yaɗa labarai na Turkiyya inda suka ruwaito cewa, tsohon shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Real Madrid ɗan ƙasar Brazil, Roberto Carlos, ya karɓi shahadar Musulunci ya.

Rahotannin sun bayyana cewa Carlos, Wanda a yanzu yake da shekaru 53, ya musulunta ne kimanin sati huɗu da suka shuɗe, bayan da ya furta Kalmar Shahada a yayin wani taro da Sheikh Jihad Hamada, ɗaya daga cikin fitattun mutane masu yaɗa addinin Allah a cikin al’ummar Musulmi a ƙasar Brazil.

Rahoton ya fito ne daga wasu jaridun Turkiyya da dama, ciki har da Haberler, inda aka bayyana cewa tsohon ɗan wasan Real Madrid da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Brazil ya karɓi Musulunci.

Ɗan wasan, Roberto Carlos ya shafe wani ɓangare na rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa yana taka leda a manyan ƙungiyoyi, ciki har da Real Madrid da Fenerbahçe, ya kuma lashe manyan kofuna a matakin kulob da kuma ƙasar Brazil.

Sai dai ya zuwa yanzu babu tabbaci kai tsaye daga Roberto Carlos da kansa kan rahotannin cewa ya karɓi Musulunci.

Wane fata za ku yi masa. Bayan shi kuma wane ɗan wasa ne kuke yi ma fatar ya karɓi shahada?

Post a Comment

Previous Post Next Post