Janye tallafin Man Fetur Shi Ne Babban Abin Alheri Da Ya Faru Da Nijeriya A Mulkin APC


Duk da cece-ku-cen da aka sha da tofin Allah tsine akan batun janye tallafin man fetur da shugaba Tinubu ya yi, tun farkon hawan mulkinsa. Yau an samu Shugaban hukumar tara Haraji ta ƙasar Nijeriya (NRS), Zacch Adedeji, ya bayyana cewa: Matakin cire tallafin man fetur da gwamnatin APC ta yi ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmad Tinubu a matsayin wani aiki mafi alheri da ya faru da Nijeriya a mulkin shugaban ƙasar cikin shekaru uku, ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya cancanci yabo kan wannan mataki, duba da irin ƙoƙarin da ya yi na jure maganganu da zagi a yayin ɗaukar wannan mataki.

Zacch Adedeji ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels TV, inda ya ce ci gaban tattalin arziƙi da gwamnati ke samu a yanzu ya samo asali ne daga matakin cire tallafin. Ya ce tsarin tallafin man fetur ya daɗe yana yi wa tattalin arziƙin Nijeriya illa, yana mai bayyana shi a matsayin tsarin da ba zai iya ɗorewa ba.

Adedeji ya ƙara da cewa, Shugaba Tinubu ba almubazzari ba ne, domin sau ɗaya yake cin abinci a yini, kuma a ƙafa yake zuwa ofis wurin aiki, mai maganar ya ƙara da cewa, shugaba Tinubu ko jirgi bai fiye hawa ba a ɗan wannan datsin saboda kula da kuma mammaƙon tattalin arziƙin ƙasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post