ASUU Ta Jami’ar Imo Ta Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba-Ta-Gani Kan Batun Jin Dadin Ma’aikata

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Imo (IMSU) da ke Owerri, ta sanar da fara yajin aiki gaba ɗaya kuma na sai baba-ta-gani, tana mai zargin gwamnatin jihar Imo da mahukuntan jami’ar da kasa aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma kan inganta jin daɗin malamai da kuma sharuɗɗan aikinsu.

Kungiyar ta sanar da fara yajin aikin ne a ranar Litinin, 10 ga Agustan 2026, yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a harabar jami’ar da ke Owerri, kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.

Shugaban reshen kungiyar, Stephen Oguji, da Sakatarenta, Lazarus Chikwendu, sun ce matakin ya biyo bayan tattaunawa da dama da suka yi da mahukuntan jami’ar, da kuma karewar wa’adin kwanaki 21 da kungiyar ta bayar ba tare da samun wani gamsasshen martani ba.

ASUU ta bayyana cewa yarjejeniyar da kungiyar da Gwamnatin Tarayya suka rattaba hannu a kai a ranar 23 ga Disamban 2025, an tsara ta fara aiki ne daga 1 ga Janairun 2026.

Kungiyar ta ce, “ASUU-IMSU ta fara yajin aiki gaba ɗaya kuma na sai baba-ta-gani daga yau, 10 ga Agustan 2026, kuma ba za ta koma bakin aiki ba har sai an aiwatar da yarjejeniyar gaba ɗaya.”

Ta ƙara da cewa, “Ci gaba da jinkirta aiwatar da yarjejeniyar ba ya haifar da wani amfani face ƙara ta’azzara rikicin masana’antu.”

Malaman sun kuma bayyana damuwa kan wasu matsalolin kuɗi da jin daɗin ma’aikata da har yanzu ba a warware ba. Waɗannan sun haɗa da rashin biyan bashin karin girma tun daga shekarar 2016, albashin watanni da dama da ake bin wasu mambobi, bashin kuɗaɗen rajistar mambobi (check-off dues) na tsawon watanni 21, da kuma rashin biyan Alawus na Ayyukan Ilimi (Earned Academic Allowance) tun daga shekarar 2009.

Haka kuma, kungiyar ta soki ci gaba da riƙe jami’ar a ƙarƙashin tsarin Asusun Bai Ɗaya na Gwamnati (Treasury Single Account – TSA), tana mai cewa hakan ya lalata cikakkiyar cin gashin kan jami’a.

A cewar kungiyar, waɗannan matsaloli ba sababbi ba ne, domin irin su ne suka haddasa yajin aiki a shekarar 2024 kafin daga bisani aka dakatar da shi bayan roƙon mahukuntan jami’ar da kuma alkawuran da suka bayar.

Kungiyar ta ce duk da abin da ta kira watsi da haƙƙoƙin jin daɗin mambobinta, malamai sun ci gaba da gudanar da aikinsu cikin ƙwazo da ƙwarewa.

Ta ce, “Abin takaici ne ƙwarai ganin cewa duk da sadaukarwar da mambobinmu suka nuna wajen gudanar da aikinsu, har yanzu gwamnatin jihar ba ta cika alkawuran jin daɗin ma’aikata da ta yi ba.”

ASUU-IMSU ta kuma bayyana cewa an riga an fara aiwatar da irin wannan yarjejeniya a wasu jami’o’in jihohi, ciki har da na Bauchi, Ekiti, Ogun, Osun da Sokoto.

Saboda haka, kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Imo da ta gaggauta ba da umarnin aiwatar da yarjejeniyar a Jami’ar IMSU.

Haka kuma ta roƙi sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, ƙungiyoyin fararen hula, iyaye, ƙungiyoyin ɗalibai da sauran masu ruwa da tsaki da su shiga tsakani domin ganin an shawo kan matsalar.

A ƙarshe, kungiyar ta jaddada cewa tana maraba da tattaunawa da shawarwari a matsayin hanya mafi dacewa wajen warware rikice-rikicen ma’aikata, amma ta gargaɗi cewa haƙurinta da neman sulhu bai kamata a ɗauka a matsayin amincewa da ci gaba da tauye haƙƙoƙin jin daɗin mambobinta ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post