Mataimakin Shugaban Amurka ya Jaddada Taurin Kan Iraniyawa

Mataimakin Shugaban Amurka, J.D. Vance, ya ce yana ganin Iraniyawa a matsayin wasu mutane masu taurin kai, inda ya ce hakan na daga cikin ƙalubalen da ake fuskanta wajen warware rikicin da ke tsakanin ƙasarsa da Iran.

A wata hira da ya yi da tashar Fox News, Vance ya mayar da martani kan sukar da wasu Amurkawa ke yi game da yadda gwamnatin ƙasar ke tafiyar da yaƙin da Iran.

Ya ce akwai rarrabuwar kawuna a cikin gwamnatin Iran, kuma wani ɓangare na shugabannin ƙasar na son a ci gaba da tattaunawa, yayin da wani ɓangaren masu tsattsauran ra'ayi ke son a ci gaba da yaƙi.

Vance, wanda ya jagoranci tawagar Amurka a tattaunawar Islamabad, yana da yaƙinin cewa daga ƙarshe "komai zai ƙare ne ta hanyar da za ta amfani al'ummar Amurka."

Sai dai ya bayyana cewa ana samun ci gaba da koma baya a rikicin da ake yi da Iran

Wasu rahotanni sun ce shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, na iya kai ziyara Pakistan cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

Sai dai gwamnatin Iran ba ta tabbatar ko musanta waɗannan rahotanni ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post