Yaƙin da ke ci gaba a Sudan na ƙara yin barazana ga Dala-dalan Meroe, wani muhimmin wurin tarihi da Hukumar UNESCO ta ayyana a matsayin Wurin Tarihi na Duniya (World Heritage Site).
Dala-dalan Meroe na ɗaya daga cikin manyan alamomin tsohuwar Masarautar Kush, kuma sun kasance muhimmin abin tarihi da ke nuna wayewar kai da al'adun mutanen yankin tun shekaru dubbai da suka gabata. Sai dai rikicin da ya daɗe yana ci gaba ya sa ana fargabar lalacewar wannan muhimmin gado na tarihi.Masana da ƙungiyoyin kare kayan tarihi sun bayyana damuwa cewa faɗace-faɗace, hare-haren makamai da rashin tsaro na iya haddasa lalacewa ko rusa wasu daga cikin waɗannan tsoffin gine-gine. Haka kuma, rashin damar isa wurin ya hana gudanar da ayyukan kulawa da kiyaye wurin yadda ya kamata.
UNESCO da sauran ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sun yi kira ga ɓangarorin da ke rikici da su mutunta wuraren tarihi da al'adu, tare da kauce wa duk wani aiki da zai jefa su cikin haɗari, kamar yadda dokokin ƙasa da ƙasa suka tanada.
Masana sun yi gargadin cewa idan rikicin ya ci gaba ba tare da an samar da zaman lafiya ba, akwai yiwuwar Sudan ta yi asarar wani muhimmin ɓangare na tarihinta da al'adunta, wanda kuma ke da matuƙar muhimmanci ga tarihin Afirka da na duniya baki ɗaya.