Najeriya Na Shirin Kara Karfafa Masana’antar Kera Kayayyakin Tsaro a Cikin Kasa

Najeriya na ƙara ƙaimi wajen ƙarfafa masana’antar kera kayayyakin tsaro a cikin gida, inda ake shirin kafa layukan samar da motocin sulke, na’urorin yaƙi da jirage marasa matuƙa (drones) da sauran kayayyakin aikin soja na musamman.

Shirin na karkashin jagorancin Kamfanin Masana’antun Tsaro na Najeriya (DICON-D7G), tare da haɗin gwiwar Eagles International for Defence Systems, da nufin bunƙasa musayar fasaha, faɗaɗa ƙarfin masana’antun cikin gida da rage dogaro da kayayyakin soji da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.

Babban Daraktan DICON-D7G, Mista Osman Chennar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa bayan ziyarar duba masana’antu da wuraren kera kayayyakin soja da ta ɗauki kwanaki biyu a birnin Alkahira na ƙasar Masar, da Ministan Ƙaramar Hukumar Tsaro, Bello Matawalle, ya jagoranta.

Chennar ya ce haɗin gwiwar zai samar da guraben aikin yi sama da 200, tare da ba wa kusan tsofaffin jami’an soja 100 damar samun aikin yi.

Kayayyakin da ake shirin samarwa sun haɗa da motocin sulke na MRAP-Buffalo U.10 da M.12, MRAP-Buffalo F-4, motar Rhino Guard GXR mai na’urar yaƙi da drones kuma wadda aka ƙera domin kariya daga rokoki masu tayar da gurneti (RPG), APC Moon PT6, GXR Phantom da BMP-2 Infantry Fighting Vehicle.

Chennar ya ce wannan ci gaba na daga cikin babbar manufar gwamnati ta gina ingantacciyar masana’antar kera kayayyakin tsaro a Najeriya, wadda za ta iya ƙira, haɗawa da kera kayayyakin soja a cikin gida.

Shirin ya zo ne a lokacin da Rundunar Sojin Najeriya ke ci gaba da karɓar motocin sulke da ake ƙerawa a cikin ƙasar, a wani mataki na ƙarfafa samar da kayayyakin tsaro na cikin gida da kuma ƙara ƙarfin aikin rundunar.

Baya ga kera motocin soja, DICON-D7G na shirin gina wata tashar jiragen ruwa ta musamman ta sojoji a Legas, domin taimakawa wajen jigilar albarkatun ƙasa, sassa da kuma kayayyakin soja da aka kammala kerawa.

Chennar ya ce tashar za ta zama muhimmiyar cibiyar jigilar kayayyaki, wadda za ta taimaka wajen samar da rarraba kayayyakin soja a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka.

Ya ƙara da cewa ana sa ran ƙaddamar da tashar cikin watanni biyu zuwa uku masu zuwa.

A cewarsa, DICON-D7G na shirin ƙaddamar da tashar sojojin a Legas, wadda idan aikin ya fara za ta samar da guraben aikin yi ga sama da tsofaffin jami’an soja 200 da kuma fararen hula fiye da 1,000.

Ana sa ran wannan sabon tsarin bunƙasa masana’antar tsaro zai haifar da fa’idojin tattalin arziki da dama, ciki har da mayar da kuɗaɗen da ake kashewa wajen tsaro cikin tattalin arzikin Najeriya, bunƙasa ƙwararrun ma’aikata da rage dogaro da masu samar da kayayyakin tsaro daga ƙasashen waje.

Kamfanin ya ce wuraren masana’antu da layukan samar da kayayyakin da ake shirin kafawa za su bai wa Najeriya damar samar wa rundunonin tsaronta kayayyakin da ake ƙera a cikin gida, musamman yayin da ake gudanar da dogayen ayyukan tsaro, tare da samar da damar da ƙasar za ta iya shiga kasuwar kayayyakin tsaro ta Afirka.

Post a Comment

Previous Post Next Post