Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar National Democratic Congress (NDC) a zaɓen 2027, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya ce ya amince ya haɗa kai da Peter Obi ne saboda kishin ƙasa, tabbatar da daidaito da kuma buƙatar kawo sauyin siyasa a Najeriya.
Kwankwaso ya kuma bayyana cewa tsoffin gwamnonin Kano, Ibrahim Shekarau da Abdullahi Ganduje, da kuma Gwamna mai ci, Abba Yusuf, sun rasa tasirinsu a siyasar jihar.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan makomar siyasar wasu tsoffin abokan tafiyarsa da suka rabu da shi. Ya yi wannan bayani ne a cikin shirin News Agency of Nigeria Personality Interview Series da aka gudanar a Abuja ranar Lahadi.
Ya ce shawarar amincewa da zama mataimakin Peter Obi a zaɓen 2027 ta samo asali ne daga buƙatar samar da daidaiton yanki, adalci da kuma sauyin dimokuraɗiyya.
Ya bayyana cewa abin da ya koya daga zaɓen 2023 ya taimaka masa wajen fahimtar Obi sosai, yana mai cewa yanzu ya gamsu cewa za su iya yin aiki tare domin amfanin ƙasar.
“Mutane suna koyo a kowace rana, shi ya sa ƙwarewa take da muhimmanci. A shekarar 2023, mun yi ƙoƙarin yin aiki tare, amma a wancan lokacin ban san Peter Obi sosai ba.
“Amma a cikin waɗannan shekaru huɗu da suka gabata, na koyi abubuwa da dama kuma na fahimci cewa Peter mutum ne da zan iya yin aiki tare da shi,” in ji shi.
Kwankwaso ya ce an cimma matsayar haɗin gwiwar ne bayan tuntubar mambobin Kwankwasiyya Movement, magoya bayan New Nigeria Peoples Party (NNPP) da kuma Obidient Movement.
Ya ce dukkan ƙungiyoyin sun amince cewa Najeriya na buƙatar tikitin siyasa mai daidaita arewa da kudu, wanda zai iya samun goyon baya daga ɓangarorin biyu.
Tsohon Ministan Tsaro ya ce matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar, raguwar yawan amfanin gona da kuma lalacewar ababen more rayuwa sun ƙara masa ƙwarin gwiwar goyon bayan tsarin siyasar da zai kawo sauyin dimokuraɗiyya.
Ya ce matsin tattalin arziki ya fi shafar manoma, musamman a Arewacin Najeriya, inda samar da amfanin gona ke ƙara zama mai wahala kuma ba ya kawo riba yadda ya kamata.
Kwankwaso ya ƙara da cewa lalacewar ababen more rayuwa a sassan ƙasar, ban da wasu wurare kamar Legas, na daga cikin dalilan da suka sa ya amince ya haɗa kai da Obi.
Ya ce halin da ƙasar ke ciki a yanzu na buƙatar irin sauyin dimokuraɗiyyar da ’yan Najeriya suka nema a shekarar 2015, yana mai cewa buƙatar sauyin ta fi zama wajibi a yanzu.
Ya bayyana tikitin Obi da Kwankwaso a matsayin haɗin gwiwar da zai samar da daidaiton yanki, ƙwarewa da kuma amana.
“Nobody, no ticket can beat our own in terms of credibility, capacity and, of course, love for the country; har ma da tausayawa talakawan da ke shan wahala a faɗin ƙasar a yau,” in ji shi.
Kwankwaso ya ce amincewarsa da zama mataimakin shugaban ƙasa ba ta kasance koma baya gare shi ba, duk da irin ƙwarewar siyasar da yake da ita, ciki har da zama mataimakin kakakin Majalisar Wakilai, gwamna, minista da sanata.
Ya ce: “Ban taɓa zama mataimakin shugaban ƙasa ba. Ina ganin wannan ci gaba ne a gare ni, duk da dukkan muƙaman da kuka ambata.”
Ya jaddada cewa shawarar tasa ta samo asali ne daga fa’idar ƙasa baki ɗaya, ba wai neman biyan buƙatar kansa ba, yana mai cewa riƙe muƙamin gwamnati ya kamata a ɗauke shi a matsayin damar yi wa al’umma hidima.
“Ni a wurina, kasancewa cikin gwamnati shi ne yin hidima. Ba dole ne in zama shugaban ƙasa ba. Ba dole ma ne in zama mataimakin shugaban ƙasa ba. Waɗannan abubuwa suna hannun Allah Maɗaukakin Sarki.
“Amma gaskiyar magana ita ce, halin da ake ciki a yau ya sa dole mutum ya kalli al’amura fiye da bukatar kansa,” in ji shi.
Ya ce yarjejeniyar da ya cimma da Obi ita ce kudu za ta samar da shugaban ƙasa na wa’adi ɗaya, daga bisani kuma tsarin siyasar ya koma ga arewa.
Kwankwaso ya kawo misalan wasu shugabannin siyasa da suka amince da muƙamin da bai kai matsayin da za su iya samu ba, ciki har da Sir Ahmadu Bello, wanda ya zaɓi ci gaba da zama Firayim Ministan Arewacin Najeriya maimakon neman zama Firayim Ministan ƙasar.
Ya ce ya kamata ’yan Najeriya su fahimci cewa ana iya yi wa ƙasa hidima ta matakai daban-daban, kamar kansila, shugaban ƙaramar hukuma, ɗan majalisa, gwamna, minista, mataimakin shugaban ƙasa ko shugaban ƙasa.
A cewarsa, ya kamata shugabannin siyasa su kasance a shirye su yi hidima a duk inda aka ga buƙatarsu, maimakon ɗaukar wasu muƙamai a matsayin waɗanda ba su kai matsayinsu ba.
Kwankwaso ya kuma yi watsi da ikirarin abokan hamayyarsa cewa tattaunawar siyasarsa da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ko wasu jam’iyyun siyasa ta dogara ne da samun tikitin takarar shugaban ƙasa ko mataimakinsa.
Ya ce tattaunawar da ya yi da Shugaba Bola Tinubu bayan zaɓen 2023 ta shafi yadda za su yi aiki tare ne, ba wai barin NNPP ko neman wani takamaiman muƙami ba.
Ya ce a baya ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar APC a zaɓe, musamman ta hanyar kuri’un da jam’iyyar ta samu a Kano a shekarar 2015, amma daga bisani ya nuna rashin jin daɗinsa da yadda shugabancin jam’iyyar ya tafiyar da al’amura bayan zaɓen.
Tsohon gwamnan ya ce amincewarsa da haɗin gwiwar Obi da Kwankwaso ta ƙara ƙarfi ne saboda abin da ya kira jajircewar Obi wajen tabbatar da adalci, gaskiya da haɗin kan ƙasa.
Ya ce tsarin zai kuma tabbatar da cewa arewa ba za ta kasance cikin hasara ba, yana mai cewa fahimtar yin wa’adi ɗaya na da matuƙar muhimmanci wajen samun amincewar magoya bayansa.
Kwankwaso ya ce yana da yaƙinin cewa Obi zai mutunta yarjejeniyar da suka cimma, kuma zai yi aiki da shi a matsayin abokin tarayya, ba wai ya ɗauke shi a matsayin “taya” kawai ba.
Ya ce ƙwarewarsa ta zama mataimakin kakakin Majalisar Wakilai, minista da gwamna ta koya masa muhimmancin bai wa mataimaka damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
A cewarsa, shugaban ƙasa ko gwamna da ya bai wa mataimakinsa muhimman ayyuka yana ƙarfafa gwamnati, domin nasarar mataimakin ita ma nasarar shugaban ce.
Ya ce saboda haka yana cikin kwanciyar hankali game da tsarin da aka tsara, kuma yana da yakinin cewa Obi zai ba shi damar bayar da gudummawa mai ma’ana wajen tafiyar da gwamnati.
Da yake magana kan yadda dangantakar siyasa ke sauyawa, Kwankwaso ya jawo hankali kan makomar wasu ’yan siyasa da a baya suke kusa da Shugaba Tinubu, amma daga bisani suka rasa matsayinsu a cikin da’irar siyasar shugaban.
Ya ambaci tsohuwar Mataimakiyar Gwamnan Jihar Legas, Kofoworola Bucknor-Akerele, da tsohon Gwamnan Jihar Legas, Akinwunmi Ambode, a matsayin misalai.
Ya ce: “Na gaya masa cewa idan na zo nan, ban ganin Bucknor. Idan na zo nan, ban ganin Ambode. Sai na fara lissafa mutanen.”
Kwankwaso ya ce ƙwarewar rayuwarsa ta siyasa ta nuna masa cewa dangantakar ’yan siyasa ba ta dawwama, domin abokan siyasa na iya nisantar juna duk da cewa sun taɓa yin aiki tare na tsawon lokaci.
Sai dai ya ware tsohon Gwamnan Jihar Osun, Cif Bisi Akande, a matsayin ɗaya daga cikin ’yan siyasar da har yanzu yake ɗauka a matsayin aboki.
Ya ce dangantakar siyasa a wasu lokuta tana kama da wadda ake samu tsakanin abokan makaranta, inda tsofaffin abokan karatu kan ci gaba da hulɗa da juna duk da bambance-bambancen da ke iya kasancewa a cikin harkokin siyasarsu.
“Ba Kano kaɗai ce irin wannan ke faruwa ba, amma ina ganin abin da ya faru a Kano ya fi zama na musamman idan aka kwatanta da sauran wurare,” in ji Kwankwaso.