Gwamnan Kebbi Nasir Idris Ya Sauya Wanda Zai Yi Masa Mataimaki a Takarar Gwamna a Shekarar 2027

Gwamnan Jihar Kebbi, Hon. Nasir Idris, ya zaɓi Alhaji Ibrahim Augie a matsayin sabon abokin takararsa na kujerar gwamna a jam'iyyar APC a zaɓen 2027, inda ya maye gurbin mataimakinsa na yanzu, wato Sanata Umar Tafida.

Alhaji Suleiman Argungu, Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar APC shi ne ya bayyana wannan saƙon a ranar Lahadi a cikin Birnin Kebbi.

Argungu ya ce an ɗauki matakin ne bisa shawarar ƙwararrun lauyoyi da suka yi nazari kan cancantar mataimakin gwamnan na yanzu.

Ya ƙara da cewa, “An sauke mataimakin gwamnan na yanzu ne daga matsayin abokin takarar Gwamna Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) a zaɓen 2027 ne bisa shawarar ƙwararrun lauyoyi.”

Duk da haka, Argungu ya bayyana cewa Tafida ya amince da matakin da jam'iyyar APC reshen jihar Kebbi ya ɗauka, yana mai jaddada cewa babu wata taƙaddama ko rashin jituwa tsakanin gwamnan da tsohon mataimakin nasa.

Daga ƙarshe Sakataren ya sanar da Alhaji Ibrahim Augie a matsayin sabon abokin takarar Gwamna Idris a zaɓen gwamnan jihar Kebbi na 2027, a jam'iyyar APC.

Argungu ya yi kira ga ‘yan siyasa, da mambobin APC da magoya bayan jam’iyyar a faɗin jihar da su amince da sauyin tare da haɗa kai domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaɓen mai zuwa.

Shi ma Gwamna Nasir Idris ya yi watsi gami da Allah wadai da raɗeraɗin da ke yawo na cewa akwai rashin jituwa tsakaninsa da mataimakin nasa.

Gwamnan ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba wa gwamnatinsa haɗin kai da goyon baya domin samun ci gaba da kuma ayyukan raya Jihar Kebbi bakiɗaya.

Sabon abokin takarar gwamnan Alhaji Ibrahim Augie ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishinan Kuɗi na Jihar Kebbi a lokacin tsohon gwamnatin Gwamna Atiku Bagudu. Ibrahim Augie ya fito ne daga ƙaramar hukumar Augie ta jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post