Runudinar Sojin Iran ta sanya kyautar $30,000 ga duk wanda ya kama ko ya kashe sojojin Amurka
Rundunar sojin Iran ta sanar da bayar da kyautar dala dubu 30,000 ga duk wanda ya kamo ko ya kashe wani soja ɗan ƙasar Amurka.
An saurari sanarwar ne daga bakin shugaban rundunar sojin Iran, Amir Hatami, inda yake cewa mutumin duk da ya kama ko kuma ya kashe wani soja ɗan ƙasar Amurka sannan ya miƙa gasar ko shi ga hukumomin Iran zai samu kyautar dala dubu 30,000, kwatankwacin Royal biliyan biyar.
Hatami ya ce an ɗauki wannan matakin ne duba da yawan buƙatun da aka samu daga mutanen da ke son bayar da gudummawar kuɗi.
Ya ƙara da cewa, idan kuma mace ‘yar ƙasar Iran ta samu yin nasarar aiwatar da hakan za ta samu ladan da ya ninka adadin da muka ambata a baya sau biyu.
Rahoton ya ce kawo yanzu babu wani bayani da ke nuna cewa Amurka ta tura dakarun ƙasar zuwa Iran yayin yaƙin da ake yi a Gabas ta Tsakiya, sai dai wani aikin ceto da aka gudanar a watan Afrilun da ya shuɗe bayan da wani jirgin saman yaƙin Amurka ya faɗi.
Shugaban rundunar Sojin Iran, bai fito fili ya bayyana wuri ko lokacin da ake sa ran farautar sojojin Amurkan za ta wakana ba.
Yaƙin Iran da Amurka ya fara ne tun a ranar 28 ga Fabrairu bayan da Amurka tare da haɗin gwiwar ƙasar Isra’ila ta kai hari kan ƙasar Iran. Bayan da suka kwashe kusan kwanaki 40 suna faɗa. sai dai daga bisani an samu tsagaita buɗe wuta a watan Afrilu. Wanda bayan nan, suka ci gaba da buɗe wa juna wuta bayan wargajewar wani shirin tattaunawar zaman lafiya da aka tsara daga baya a watan Yuni.
Tun daga lokacin, Iran da Amurka ke ci gaba da musayar hare-hare lokaci bayan lokaci, musamman a kudancin Iran da yankin mashigin ruwan Hormuz.