Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya taya Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, murnar sake lashe zaben gwamna, tare da bukatarsa da ya ci gaba da samar da kyakkyawan shugabanci.
Obasanjo ya yi wannan kira ne a ranar Litinin yayin da ya kai wa Adeleke ziyarar taya murna a gidansa da ke garin Ede.
Kakakin gwamnan, Olawale Rasheed, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Osogbo.
Tsohon shugaban kasar ya kuma yi wa Adeleke addu’ar samun karin nasara, tare da bukatarsa da ya ci gaba da jajircewa wajen inganta rayuwar jama’a da samar da romon dimokuradiyya.
“Ku ci gaba da samar da kyakkyawan shugabanci, ku kuma ci gaba da biyan bukatun al’ummarku,” in ji Obasanjo.
A nasa bangaren, Adeleke ya gode wa Allah da kuma al’ummar Osun, inda ya sha alwashin ci gaba da yi wa jama’ar jihar hidima cikin gaskiya da amana.
Ya ce, “Baba, na gode da wannan ziyarar bazata. Na yi alkawarin ba zan taba kunyatar da Allah, al’ummar Osun da duk masu son dimokuradiyya da suka taimaka wajen tabbatar da wannan nasara ba.”
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar ranar Asabar, bayan ya samu kuri’u 511,067.
Dan takarar jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, ya zo na biyu da kuri’u 444,815, yayin da dan takarar African Democratic Congress (ADC), Najeem Salaam, ya zo na uku da kuri’u 17,180.
