Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da sabuwar ƙara ta tauye haƙƙin ɗan Adam kan Hukumar ICPC, inda yake neman Naira biliyan 10 a matsayin diyya bisa zargin hana matarsa da ɗansa ziyartarsa yayin da ya ke tsare.
A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1852/2026, wadda aka shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar 13 ga Agusta, El-Rufai ya yi zargin cewa ICPC ta hana matarsa, Aichatou Asabe, da ɗansa, Abba El-Rufai, ziyartarsa.
El-Rufai, ta hannun lauyansa Ubong Akpan, ya kuma haɗa shugaban ICPC da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya a matsayin waɗanda ake ƙara, na biyu da na uku.
El-Rufai ya gabatar da buƙatu guda tara, ciki har da neman kotu ta tabbatar da cewa haƙƙoƙinsa na ɗan Adam da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ya tanada, har yanzu suna aiki duk da cewa yana tsare.
Ya yi zargin cewa yadda ake ci gaba da hana iyalinsa ganinsa, musamman domin kai masa abinci, magunguna da sauran abubuwan buƙata, ba tare da ingantaccen dalili na doka ko umarnin kotu ba, ya take haƙƙoƙinsa da Kundin Tsarin Mulki ya ba shi.
Ya kuma yi zargin cewa jami’an ICPC sun hana, tare da tsoratar da matarsa da ɗansa a ranar 7 ga Yuli, lamarin da ya bayyana a matsayin tsoma baki ba bisa ƙa’ida ba cikin alaƙar aurensa da iyalinsa.
El-Rufai ya nemi kotu ta bayyana cewa ci gaba da hana shi ganawa da iyalinsa ba tare da ikon doka ba ya saba wa kundin tsarin mulki kuma ya zama aikin da ba shi da inganci a doka.
