Sanatan Kano Ta Tsakiya Ya Bayyana Ficewarsa Daga Jam'iyyar NDC Nan Take

Sanatan Kano ta tsakiya kuma mataimakin mai tsawatar da marasa rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Hon. Dr. Rufai Sani Hanga, ya sanar da ficewar tasa daga jam'iyyar adawa ta NDC.

An hango saƙon ficewar tasa ne daga jam'iyyar ND a cikin wata wasiƙar murabus mai ɗauke da kwanan wata 3 ga Agusta, 2026, wadda ya aike wa shugaban jam'iyyar na mazaɓar Dakata da ke ƙaramar hukumar Nasarawa ta Jihar Kano, Hanga ya ce murabus ɗin nasa zai fara aiki ne nan take.

Hanga ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne bayan dogon nazari da tunani mai zurfi, ya ci gaba da cewa ya bar jam'iyyar ne domin mayar da hankali kan wasu al'amuran rayuwarsa da kuma ci gaban aikinsa.

Sanata ya miƙa godiyarsa ga shugabannin jam'iyyar a matakin mazaɓa, kwamitin gudanarwa da ɗaukacin mambobin NDC bisa irin goyon bayan da suka ba shi, gami da haɗin kai da suka ba shi a lokacin da yake cikinta.

Hon. Rufa'i kuma ya buƙaci a cire sunansa daga kundin rajistar mambobin jam'iyyar a matakin mazaɓa, tare da bayyana cewa ya mayar da katin shaidar zama ɗan jam'iyyar NDC a cikin takardar da ya aike da ita.

Sanatan ya yi fatan alheri ga jam'iyyar da mambobinta tare da fatan nasara ga dukkan ayyukansu na gaba. Sai dai, a cikin wasiƙar da ya aike ta yin murabus daga jam'iyyar, Hanga bai bayyana wata jam'iyyar siyasa da yake da ƙudirin komawa ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post