Tarihin Macen Da Ta Fi Kowace Mace Haihuwa A Duniya

Macen da tarihi ya kiyaye a matsayin wadda tafi kowacce yawan haihuwa itace Mrs Vassillev ta birnin Moscow a kasar Rasha, wadda ta rayu tsakanin shekarun 1707 - 1782. Ance tayi nakuda sau 27, sau 16 tana haihuwar tagwaye, ta haifi 'yan uku sau bakwai, ta haifi 'yan huɗu sau huɗu. Jimilla ta haifi 'ya'yaye 69 reras.. (Kimiyya ta tabbatar da haka). Ita ce matar farko na Feodor Vassilyev.

Mrs Vassillev

An rubuta labarin ta cikin tarihi, ciki har da makarantar Moscow Academy of Science, kuma an gabatar da ita ga Sarauniyar Rasha Catherine The Great. Yayin da labarinta ya kasance batun tattaunawa da shakku, labarinta ya ci gaba da zama tarihi mai ban mamaki a cikin haife-haifen ɗan adam. Daga baya mijin nata ya sake yin aure ya kuma haifi ‘ya’ya 18 tare da matarsa ta biyu, wanda ya kai adadin ‘ya’yansa 87.

Post a Comment

Previous Post Next Post