Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC daga yankin Sanatan Kogi ta Gabas sun kai wa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ziyarar godiya a gidansa da ke Abuja.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin ɗan takarar APC na kujerar Sanatan Kogi ta Gabas, Dakta Joseph Erico, ta ce ta kai ziyarar ne domin nuna godiya ga Yahaya Bello bisa jagoranci, goyon baya da shawarwarin da ya ba su kafin da bayan zaɓen fidda gwani na jam'iyyar, wanda ya haifar da fitowar Erico a matsayin ɗan takara.
Da yake jawabi a madadin tawagar, Hon. Edime Edime ya yabawa Yahaya Bello kan ƙoƙarinsa na tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya a cikin APC da kuma jihar Kogi.
Ya ce jagorancin tsohon gwamnan ya taimaka wajen ƙarfafa haɗin kan jam'iyyar da kuma zaman lafiya tsakanin al'ummomin jihar.
A nasa jawabin, Yahaya Bello ya gode wa tawagar bisa ziyarar tare da taya Dakta Joseph Erico murnar zama ɗan takarar APC na kujerar Sanatan Kogi ta Gabas.
Ya kuma buƙaci mambobin jam'iyyar su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai tare da ƙara zage damtse wajen tattara goyon bayan jama'a domin samun nasara a zaɓuka masu zuwa.
Hakazalika, Bello ya yi kira ga mambobin APC da su ci gaba da mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Ahmed Usman Ododo baya domin ci gaban jihar Kogi da Najeriya baki ɗaya.
