Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya fara hutun mako biyu a ranar Alhamis bayan samun amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Wannan shi ne hutunsa na farko tun bayan da ya hau mulki tare da shugaban ƙasa a ranar 29 ga Mayu, 2023.
A cikin wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Stanley Nkwocha, ya fitar, an bayyana cewa Shettima zai yi amfani da lokacin hutun ne wajen nazari, yin tunani da kuma ƙara ilimi domin ƙarfafa ƙwarewarsa wajen ci gaba da yi wa ƙasa hidima.
Nkwocha ya ce hutun zai ba Mataimakin Shugaban Ƙasa damar yin bitar shirye-shiryen gwamnatin da ke gudana, ƙara fahimtar sabbin manufofin ƙasa da na duniya, tare da shirya kansa domin nauyin ayyukan da ke gaba yayin da gwamnatin tarayya ke ƙara himma wajen aiwatar da ajandar Renewed Hope.
Sanarwar ta ce tun bayan da ya hau ofis, Shettima ya taka muhimmiyar rawa wajen daidaitawa da sa ido kan muhimman shirye-shiryen gwamnati, musamman a fannonin bunƙasa tattalin arziki, samar da wadataccen abinci, ayyukan jin ƙai, sauyin fasahar zamani, samar da ayyukan yi da kuma haɗin gwiwar yankuna.
Haka kuma, shi ne shugaban Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa (National Economic Council), wadda ta haɗa gwamnoni 36 na jihohin Najeriya, Gwamnan Babban Bankin Najeriya da sauran manyan jami’an gwamnati domin tattauna manufofin tattalin arziki da walwalar al’umma.
Shettima ya kuma wakilci Shugaba Tinubu a manyan tarukan ƙasa da ƙasa da na yankuna. Daga cikin su akwai tarukan G20 da AU-EU da aka gudanar a watan Nuwamban bara, da sauran muhimman tarukan ƙasa da ƙasa, musamman lokacin da Shugaba Tinubu ya zaɓi ci gaba da zama a cikin ƙasa saboda matsalar sace-sacen mutane da ta ƙamari a Papiri da ke Jihar Neja da kuma Eruku a Jihar Kwara.
Nkwocha ya jaddada cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa na ci gaba da jajircewa kan ƙa’idojin aminci, nauyin aiki da hidimar ƙasa da suka kasance ginshiƙan rawar da yake takawa a gwamnatin, tare da ci gaba da mara wa shugaban ƙasa baya wajen gina Najeriya mai tsaro, wadata da ci gaba.
Ana sa ran Shettima zai koma bakin aikinsa bayan cikar hutun mako biyu, a ranar 20 ga Agusta, 2026 ko kuma kusa da wannan lokaci.