Bayan shafe tsawon shekaru 10 sun akurɓar soyayya. Cristiano Ronaldo ya cika alƙawarin da ya ɗauka na cewa, bayan kammala wasannin cin kofin duniya na shekarar 2026 wanda ya gudana a ƙasashen Amurika da Canada da kuma Mexico zai angwance da masoyiyar tasa Georgina Rodriguez.
Ronaldo da Georgina dai sun fara haɗuwa ne a garin Madrid a shekarar 2016 a wani shafi da take kasuwanci, wanda tun daga nan ne suka fara soyayya, wadda har ya kai su ga sun samu 'ya'ya a tsakaninsu.
Bayan tsawon lokaci Georgina da Ronaldo sun yi baiko a shekarar da ta gabata wato 2025. Wanda kuma nan ba da jimawa ba za a yi gagarumin taron ɗaurin auren nasu a garin da aka haifi Cristiano Ronaldo wato Funchal, a cikin Majami'ar Cathedral da ke Funchal da ke tsibirin Madeira na ƙasar Portugal. Wanda ya zuwa yanzu jaridar BBC ta ruwaito cewa, har ma an kama babban otel ɗin nan mai suna Savoy Palace domin fara gudanar da shirye-shiryen bikin.
Georgina da Ronaldo a zamansu na tsawon shekaru goma zuwa yanzu sun haifi 'ya'ya 5, Alana Martina wanda aka haifa a shekarar 12 ga watan Nuwamba 2017, sai kuma ta ƙara haihuwar tagwaye, Bella Esmeralda da kuma Angel a 18 ga Afrilu a shekarar 2022, wanda Angel ya rasu a wajen haihuwa.
Amma duk da haka, tana rainon yaran Ronaldo guda 3, wato Cristiano Ronaldo Jr Wanda aka haifa a shekarar 2010 sai kuma wasu tagwaye da aka haifa masa a ranar 8 ga Yuni na shekarar 2017 masu suna: Eva Maria da kuma abokin tagwaicinta Mateo Ronaldo.
Da fatan za ku samu halartar wannan gagarumin buki da za a yi a Funchal, Ni ma kan na yi alƙawarin matuƙar Ronaldo ya gayyace Ni ta hanyar kiran lambar wayata to lallai ba za a barin a baya ba. Ka da ka bari a ba ka labari, domin buki ne da zai tara manyan 'yan ƙwallo daga ko'ina a faɗin duniya musamman ma ƙasashen da shi Ronaldo ya taka leda da suka haɗa da: Ingila da Sifaniya da Italiya har ma da Saudi Arabia inda yake taka leda a yanzu.
Sai kun zo