Da tsakar ranar yau ne dai, aka samu labarin shugaban ƙasar Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin gaggawa ga Hukumar EFCC da ta yi gaggawar komawa kotu a sake lalen dokar da ta ba wa hukumar damar garƙame asusun jihar Osun.
Hukumar EFCC ta samu sahalewar kotu ne a ranar Laraba 5 ga watan Agusta domin rufe asusun ajiyar gwamnatin jihar ta Osun, duk da ƙaratowar zaɓen jihar da za a yi a wannan Asabar ɗin mai zuwa.
Sai dai hukuncin da Kotun haɗi da hukumar suka zartar bai yi wa Shugaban ƙasa daɗi ba, duba da cewa ana ta nuna yatsan a kansa, har ma wasu na ganin duk wani umarni ko aiki da wata ma'aikata ta tarayya ta yi, ana mayar da shi kai tsaye ga shugaban ƙasa. Wannan ne ya sa, ya bayar da umarnin a gaggauta komawa kotu domin a warware wannan hukunci sannan a sakar masu aljihun asusun ajiyar jihar domin ci gaba da shirye-shiryen zaɓen da ke gabansu.
Wannan umarnin ne ya sa, shugaban adawa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC Alhaji Atiku Abubakar kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, ya buga ƙasa tare da faɗin cewa. Lallai ya kamata Shugaban ƙasa ya sa baki a fito da Malam Nasiru El-Rufa'i daga hannun hukumar ICPC da yake tsare tsawon makonni, tun da dai har yana da ikon yin hakan, domin ga shi ya yi an gani.