Sufeto Janar na ’yansandan Nijeriya, Tunji Ɗisu, ya yi babban gargaɗi ga ’yan siyasa da su guji yin amfani da matasa wajan ba su makamai da kayan maye domin amfani da su wajen yaƙar abokan hamayyarsu gabanin zaɓen 2027.
Ɗisu ya yi wannan jan kunnen ne a ranar Alhamis 19/08/2026 a Abuja, yayin wani taron tattaunawar shugabancin matasa da tsaro na ƙasa, wanda rundunar ’yansandan Nijeriya ta shirya domin bikin Ranar Matasa ta Duniya ta 2026.
Ya kuma ƙara da cewa, rundunar ba za ta lamunci tashin hankali, ko amfani da makamai a harkokin zaɓe da tsoratar da masu kaɗa ƙuri’a ko lalata dukiyoyin al'umma ba.
Ɗisu ya buƙaci shugabannin siyasa da kada su ɗauki matasa, su ba su makamai ko su ɗauki nauyin tashe-tashen hankula. Ya ƙara da cewa aikata irin waɗannan laifukan na iya lalata makomar ƙasar.
IGP ya kuma yi gargaɗi kan tashin hankalin siyasa da ke faruwa a kafafen sada zumunta, musamman waɗanda suka haɗa da, yaɗa labaran ƙarya da kalaman ƙiyayya da cin zarafi ta yanar gizo da yin kwaikwayon mutane.
Shugaban 'yansandan ya shawarci matasa da su tabbatar da sahihancin bayanan da suke samu a kafafen sadarwa kafin su fara yaɗa su, ya kuma yi kira da su kauce wa abubuwan da ka iya haddasa rikici ko tashin hankali yayin kamfen na siyasar.
Bayanan na Ɗiso na zuwa ne jim kaɗan bayan da aka samu rahotannin kashe-kashe da hare-haren da suka biyo bayan zaɓen gwamnan Jihar Osun na baya-bayan nan, da aka yi ranar Addabar, inda jam’iyyun Accord da APC suka rasa wasu daga cikin mambobinsu.
Daga cikin waɗanda rikicin ya haɗa da su, har suka rasa rayukansu sun haɗa da: Dele Ayegbo, ɗan'uwan Wole Oke, Daraktan Janar na yaƙin neman zaben APC a jihar, wanda rahotanni suka ce an harbe shi kwanaki biyu kafin zaɓen.
Duk da haka, rundunar ’yansandan ƙasar ta dage kan cewa wasu daga cikin rikice-rikice da kashe-kashen da suka faru gabanin zaɓen Osun, suna da alaƙa ne da ƙungiyoyin asiri ba wai rikicin siyasa ne kai tsaye ba.